MARTANI GA BAKARE: Buhari ba zai fidda ‘halifan’ sa a zaben 2023 ba

0

Fadar Shugaban Kasa ta maida wa Tunde Bakare raddi cewa Shugaba Muhammadu Buhari ba zai fidda wani dan takara daya ya ce shi ne zai gaji kujerar sa a zaben shugaban kasa na 2023 ba.

Kakakin Yada Labarai na Buhari, Femi Adesina ya ce duk da Buhari zai so a zuciyar sa a ce ga wanda zai gaje shi, “to ba zai fidda wani ya ce shi zai zama ‘halifan sa’ ba.”

PREMIUM TIMES ta buga labarin da Tunde Bakare ya shawarci ya shawarci Buhari ya fito da wanda ya ke so ya gaje shi a zaben shugaban kasa na 2023 da APC za ta tsaida takara, idan lokacin ya zo.

Bakare ya ce shugabannin kasashe irin su China, Singapore da Afrika ta Kudu duk su na fidda wanda zai gaje su tun kafin su kammala wa’adin su a kan mulki.

“Mu koyi darasi daga Nelson Mandela, wanda kafin ya sauka daga wa’adin zango daya, sai da ya tsaida Thabo Mbeki da Cyril Ramaphosa.”

Haka Bakare ya buga misali a shawarar da ya bai wa Buhari.

Bakare ya yi takarar shugaban kasa tare da Buhari a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa na Buhari, a zaben 2011.

Shi ne kuma Shugaban Cocin Latter Rain Assembly.

A martanin da ya bayar, Adesina ya yi magana a gidan talbijin na Channels ya ce, “Da yardar Allah cikin watan Mayu, 2023 Buhari zai kammala wa’adin sa na biyu, kuma wanda shi ne na karshe. Ba zai sake tsayawa takara ba. Wannan shi ne shirin da ke cikin zuciyar sa.

“Fasto Bakare y ace kamata ya yi Buhari ya bayyana wanda ya ke so ya gaje shi. Amma dai ba zai yi hakan ba. Ba kuma zai yi katsalandan a cikin tsarin da ya kamata a fitar da wanda zai fito takarar bayan sa ba.

“Shugaban Kasa ba zai fidda wanda zain zama ‘halifan sa’ ba. Mun san shi, ba irin mutanen da aa su wannan katsalandan din ba ne.

“Amma dai zai shiga tsamo-tsamo ya tabbatar da cewa an bi ka’idar duk da ta dace wajen yin zabe sahihi, ingantacce kuma karbabbe, wanda babu wanda za a bari ya shigo ya yi amfani da makudan kudade domin ya yi babakere ya zama dan takara.”

Adesina ya ce Buhari ba zai mika mulki ba ga wadanda za su maida Najeriya mugun halin da aka fiddo ta a ciki ba, ko kuma wadanda za su sake wawure dukiyar ba.

“A’a, hakan ba zai taba yiwuwa ko faruwa ba.”

Share.

game da Author