Majalisar Tarayya ta nemi Buhari ya tsige Buratai da sauran Manyan Hafsoshi

0

Ranar Laraba Majalisar Tarayya ta yi kira ga dukkan Manyan Hafsoshin Sojoji da su gaggauta yin murabus, ko kuma su nemi Shugaba Muhammadu Buhari ya gaggauta tsige su.

Dan Majalisar Tarayya Abubakar Fulata, wanda ke wakiltar Kananan Hukumomin Birniwa, Guri da Kiri-Kasamma ne ya gabatar da batun neman tsige su din.

Ya ce dukkan su sun gaza wajen tabbatar da nasarar ayyukan da aka dora musu.

Ya ce babu wani amfanin da za a rika maimaita abu daya, alhalin ko sau nawa aka maimata a baya, babu wani da mai ido da maimaitawar ta haifar.

“A yi ta maimaita abu daya, ba tare da canji ba, kuma babu wata nasara, wannan ai “hauka ne.”

“Ko wa’adin lokacin su yak are, ko ma bai kare ba, to su sauka kawai.” Inji Honorabul Fulata.

Wadanda aka nemi su yi murabus din, sun hada da Babban Hafsan Tsaron Kasa, Abayomi Olonisakin, Babban Hasfan Sojoji, Tukur Buratai, Babban Hafsan Sojojin Ruwa, Ibok-Eke Ibas da kuma Babban Hafsan Sojojin sama, Sadique Abubakar.

Dukkan su Buhari ya nada su a cikin watan Yuli, 2025.

Sai dai kuma Buhari ya ci gaba da aiki da su, duk kuwa da cewa wa’adin su duk ya cika, sai Buhari ya kara musu wasu shekarun bayan ya sake ci zabe a cikin 2019.

Dama kuma a ranar Laraba din ce Sanata Eyinyire Abariba ya yi kira ga Shugaba Buhari da ya sauka, saboda kasa shawo kan matsalar tsaro, kusan shekaru biyar da hawa mulkin sa.

Share.

game da Author