Majalisa za ta gyara doka domin halasta kafa Amotekun

0

Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila, ya bayyana cewa majalisa za ta yi wa Kudin Tsarin Mulkin Najeriya, domin a halasta kungiyoyin tsaro na sa-kai a fadin kasar nan.

Femi ya yi wannan bayanin a ranar Laraba, lokacin da ya ke jawabin fara bude zaman majalisa.

Kakakin ya yi wannan sanarwa ce a daidai lokacin da Najeriya ta rukume da gardandamin rudanin kafa Dakarun Amotekun da jihohin Yarabawa suka yi a farkon Janairu.

An dai kaddamar da Amotokun a karkashin hadin guiwar jihohin Oyo, Ondo, Ogun, Osun, Ekiti da kuma Lagos.

Bayan kaddamar da dakarun ne gwamnatin tarayya ta hannun Ministan Shari’a Abubakar Malami ya bayyana cewa haramtacciyar kungiya ce, domin babu wata doka daga majalisar jiha ko ta tarayya da ta halasta kafa dakarun.

Bayan hayaniya ta yi zafi, gwamnonin jihohin Kudu Maso Yamma sun gana da Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, inda a karshe aka cimma matsayar cewa a yi wa gabadaya shirin kafa Amotekun garambawul, ta yadda zai samu karbuwa.

A nasa jawabin a ranar Laraba, Femi Gbajabiamila ya ce dalilin kafa Amotekun ya taso ne saboda matsalar tsaron da ake fama da ita a fadin kasar nan.

Dama kuma a wannan makon Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya bayyana cewa kafa Amotekun ba wani shiri ko kulli ko tuggu ba ne na ballewa daga Najeriya.

Shi ma jagoran APC, Bola Tinubu, ya yi magana a kan kafa Amotekun.

Arewa an kafa wasu kungiyoyi da masu goyon bayan kafa Amotekun suka ce bas u da wani bambanci da Dakarun Amotekun.

Kungiyoyin da aka kafa din sun hada Hisbah, CJTF da sauran su.

Share.

game da Author