A ranar Alhamis ne manajan ofishin MTN Ibrahim Dasuki ya bayyana wa manema labarai cewa ‘yan fashi da makami guda Uku sun afka wa ofishin dake jihar Kebbi sannan sun sace Naira miliyan 4.5.
Dasuki ya ce ‘yan fashin sun afka wa ofishin MTN dinne da rana tsaka inda suka da misalin karfe Uku na rana.
Ya ce sun shigo harabar ofishin a cikin mota kirar ‘Tayota Salon’ rike da bindigogi kirar ‘AK47’.
“Nan da nan suka sa kowa ya kwanta a kasa sannan biyu suka shiga cikin ofis din.
Dasuki ya ce cikin minti Biyar ‘yan fashin sun tafi da Naira miliyan 4.5.
“Ga dukan alamu wadannan ‘yan fashi sun biyo sakon wani ma’aikaci ne da aka yi ya je ya ciro wadannan kudade domin aiki da su da za a yi a ofishin.
‘Yan sanda sun ce za su bi sawun wadanda suka aikata wannan abu domin a kamo su.
Discussion about this post