A ranar Litini ne ma’aikatan asibitin FMC dake Jabi Abuja kuma mambobin kungiyar likitoci ta (ARD) suka fara yajin aikin kwanaki uku.
Shugaban kungiyar ARD reshen babban birnin tarayya Adejo Arome ya sanar da haka ta yawar tarho wa PREMIUM TIMES.
Arome ya ce likitocin sun yi haka ne domin bai wa asibitin lokaci ta biya su albashin su da aka rika zaftarewa a shekarar 2019.
“Mun samu labarin cewa gwamnati ta biya asibitin wadannan kudade amma asibitin ta ki biyan ma’aikata.
“Asibitin mu ta tabbatar mana da cewa an biya wadannan kudade amma kudaden na yin wasu aiyukka ne a asibitin bana walwalan ma’aikata ba.
“Ga dukkan alamu mahukunta a asibitin sun barnatar da kudaden mu shine ya sa muka fara wannan yajin aiki.
“Sannan ba wai asibitin bata da isassun kudaden da za ta biya mu hakkunan mu bane kawai ganin dama ne na su.
Arome ya ce likitoci za su komo aiki ne da idan asibitin ta biya wadannan kudade.