Ministan Yada Labarai Lai Mohammed, ya bai wa Hukumar Kula da Gidajen Radiyo da Talbijin ta Kasa, NBC umarnin ta gaggauta fito da ka’idojin da za a kakaba wa jaridun ‘online’ na kasar nan.
Sannan kuma ya ce ya fito da hanyar takure kafafen yada labarai na kasashen waje yadda za su kasa watsa bayanai da kuma kalaman kiyayya a cikin Najeriya.
Baya ga wadannan, Lai ya kara bada umarnin fito da watsu tsarbace-tsarbace na sa-ido, kwaskwarima da sauran su.
Wannan umarni na kunshe a cikin wata takarda da jami’in yada labarai na minista, Segun Adeyemi ya sa wa hannu a madadin ministan, a yau Alhamis.
Idan ba a manta ba, cikin watan Oktoba, 2018, Lai ya bayyana cewa Hukumar NBC za ta fito da ka’idojin kakaba wa jaridun n’online’ takunkumi, dabaibayi da tarnaki a kasar nan.
Ya ce ya na so a shimfida ka’idojin da kafafen za su rika samar da aikin yi a kasar nan.
Daga nan ya kara da cewa dukkan wadannan kafafen watsa labarai za kuma a tabbatar cewa bayanan da suke wtsawa kashi 70 bisa 100 duk na kasar nan ne ba na kasashen ketare ba.
“Ana so kuma a tabbatar duk wanda ya saka talloli a kafafen yada labarai masu zaman kan su kamar radiyo, talbijin da sauran nau’o’in sadarwa ya biya, kuma ana saka tallolin kayayyakin gida.
“Kuma gwamnati za ta rika cajar wasu kudi idan an sa tallolin, domin yin amfani da kudin a inganta da habbaka kafafen yada labaran.”
Minista ya ce za a sa ka’ida cewa a daina daukar sautin kida ko wakar wani haka kawai ana amfani a radiyo da talbijin ko wasu kafafen yada labarai kyauta, ba tare da biyan kudi ba.