KWAYOYIN CUTAR CORONA: Hukumar NCDC ta tsaurara matakai a tashoshin Najeriya

0

Hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ta tsaurara matakai a tashoshin jiragen sama da ruwan Najeriya domin yin rigakafin kada a shigo Najeriya da kwayoyin cutar ‘CORONA VIRUS.’

Hukumar ta dauki wannan mataki ne domin kauce wa fadawa cikin halin kakanikayi tun bayan barkewar cutar a kasar Chana inda mutane bakwai suka rasu sannan aka gano wasu mutane 500 dauke da kwayoyin cutar.

Rahotanni sun nuna cewa cutar da yadu zuwa kasashen Amurka, Korea ta Kudu,Thailand, Japan da Asutralia.

NCDC ta yi kira ga matafiya da su tabbatar sun yi gwajin wannan cuta a wuraren yin gwajin cutar da hukumar ta kebe a tashoshin jiragen saman kasar nan.

KWAYOYIN CUTAR CORONA

Dabbobi ne ke dauke da Kwayoyin cutar ‘Corona Virus’ amma kuma idan ya harbi mutum sai ya zama matsala.

Dabbobin kamar su mage, kare, rakumi da jemage.

Mutum na iya kamuwa da cutar idan yawan yana mu’amula da dabobbi da kuma wanda ya riga ya kamu da cutar.

Alamun cutar sun hada da zazzabi, mura, rashin iza numfashi yadda ya kamata, tari,rashin iya cin abinci da sauran su.

HANYOYIN GUJEWA KAMUWA DA CORONA VIRUS.

1. A guji yawan cudanya da dabobbi.

2. Wanke hannu da ruwa da sabulu na da mahimmanci musamman bayan an taba dabbobi.

3. A rage yawan zama kusa da wadanda suka kamu da cutar.

4. A tabbata hannu na da tsafta kafin a taba ido, baki da hanci domin gujewa kamuwa da cutar.

Share.

game da Author