Da sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai
Dukkan kyawawan yabo da godiya sun tabbata ga Allah. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad (SAW), da Iyalan sa da Sahabban sa baki daya.
Ya ku ‘yan uwa, a lokacin da wasu daga cikin wawayen ‘yan siyasar arewa suka zamanto basu da wata himma ta kawo wa jama’ar su yanci da walwala kawai sai tunanin 2023, a lokacin da suke ta fadi tashi da kokarin ganin sai sun ga bayan yankin na arewa, a kokarin su na ganin cewa sai sun jefa yankin cikin rudani da hayaniya, ta hanyar sayar da mutuncin ‘yan arewar ga wasu ‘yan siyasar kudu da ‘yan kudade kadan da za su sanya a aljihun su, sai gashi kwatsam, kungiyar nan ta rikakkun ‘yan ta’adda wadda ke ikirarin cewa tana fafutukar yin jihadi, wadda aka fi sani da suna Ansaru, ta fito fili karara ta dauki nauyin alhakin harin da aka kaiwa baban mu, wato mai martaba Sarkin Potiskum, a ranar talatar da ta gabata, a kan hanyar sa ta Kaduna zuwa Zariya. Harin da yayi sanadiyyar mutuwar akalla kusan mutum talatin daga cikin tawagar Sarkin, kamar yadda rahotanni suka nuna. Kungiyar ‘yan ta’addan ta Ansaru ta bayyana wannan ikirari na ta ne a kafar yada labarai ta al-Qaidah mai suna Thabat News Agency.
Ya ku jama’ah, a cikin wannan lokaci da muke na tashin hankali da damuwa da jarabawa iri-iri; lokacin da arewa ke neman hadin kai da dunkulewa wuri guda domin tunkarar wadannan fitintinu; yankin da dama can yayi kaurin suna wurin maganar masu satar mutane domin neman kudin fansa, ‘yan fashi da makami, barayin shanu, Boko haram, shaye-shaye a tsakanin matasa maza da mata, rikice-rikicen addini da na kabilanci, talauci, rashin aikin yi, jahilci, matsalar almajirci da dai sauran su; a daidai wannan lokaci ne kuma muke fuskantar wani irin sharri da munafunci daga wasu batagarin ‘yan siyasar arewar. A inda muke da cikakken labari da rahoto na gaskiya, wanda babu karya a cikin sa, cewa, wasu ‘yan siyasar mu sun gama shiri tsaf, domin sayar da yankin ga wasu ‘yan siyasar kudu. Wadannan ‘yan siyasa, kamar yadda kuka sani, wallahi ba yankin na arewa ne a gaban su ba. Kawai abunda yake gaban su shine aljihun su! Wanda in dai har zasu samu kudi, to ba yankin arewa ba ko jama’ar su, wallahi ko iyayen su suna iya sayarwa su samu kudi!
Ya ku jama’ah, kowa dai yana sane da irin fadi-tashin da masu Martaba, sarakunan mu na arewa suke yi na ganin yankin ya samu zaman lafiya da yaduwar arziki mai dorewa. Kuma kowa yasan irin gudummawa da wadannan bayin Allah, wato sarakuna suke bada wa domin samar da zaman lafiya a yankin mu na arewa mai albarka. Zamu fahimci hakan, ta duba da irin yadda al’ummah da talakawa suke yin tururuwa zuwa gidajen sarakunan domin a warware masu matsalolin su na rigingimu daban-daban, da matsaloli na rayuwar yau da kullum, irin tururuwar da ba zaka taba samu ana yiwa wani gwamna daga cikin gwamnoni ba, domin yau ina ma talakawan za su ga gwamnan bare har sukai koke-koken na su gare shi?
Duk da haka, da dukkan irin kalubale daban-daban da wadannan sarakuna suke fuskanta, har daga bangaren ‘yan ta’adda, kamar yadda ya faru da mai Martaba Sarkin Potiskum, da ma Sarkin Goza da ‘yan ta’adda suka taba kashewa a baya, da harin da ‘yan ta’adda suka taba kai wa Mai Martaba Sarkin Kano, marigayi Ado Bayero, da Sarkin Kano na yanzu, Malam Muhammadu Sanusi II, amma wai abun mamaki, har yanzu akwai wasu daga cikin ‘yan siyasar da basu san girma da darajar sarakunan nan ba!
Kwanan nan nike samun labari daga majiyoyi masu karfi, wadanda babu wasa a tare da su, cewa wai hatta Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III bai tsira daga irin wannan iyashege da rashin mutunci na wasu batagarin ‘yan siyasa ba. Wai sun yi shirin cewa da ace mai girma gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya fadi a shari’ar da aka yanke ta kotun koli, kuma dan takarar su ya hau gwamna, to da irin cin mutunci da wasu suke yiwa sarakunan su, suma haka zasu yi wa Mai Alfarma Sarkin Musulmi. Sai ga shi ta Allah ba tasu ba, Tambuwal din ne yaci nasara a kotu. Da ace wadannan mutane sun ci nasara, da bamu san irin laifi ko karyar da su kuma zasu kirkiro suce Sarkin Musulmin yayi ba. Domin wannan kadan ne daga cikin ayukkan su. Kai jama’ah, wallahi ni ban ma san dalilin da yasa wasu ‘yan siyasa, musamman ma na arewa, basu san girma da darajar sarakunan mu ba? Yanzu don Allah a wannan yanayi da muke ciki, bai zama wajibi wadannan ‘yan siyasa su nemi hadin kan sarakunan su domin shawo kan wannan matsalolin na rashin tsaro da arewa ta ke fuskanta ba? Shin akwai wani lokaci da yankin arewa yake bukatar zaman lafiya da hadin kai da ya wuce wannan lokaci na jarabawa iri-iri?
Don Allah ku dubi wani abun mamaki, abun dariya, wani dan barandar wadannan ‘yan siyasar, marar aikin yi, mai neman na tuwo a wurin ‘yan siyasar, ya fito yana yada karya da sharri, yana yiwa mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II kazafi, wai yana cewa a lokacin da mai girma shugaban kasar Najeriya, shugaba Muhammadu Buhari yayi tafiya jinya kasar waje, lokacin da Allah ya jarabe shi da rashin lafiya, wai Sarkin na Kano ya samu mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, yace da shi, yana roko a dauke shi mataimakin shugaban kasa idan shi Osinbajo ya dare kan gadon mulkin Najeriya, wai saboda shi Sarkin yana ganin cewa shugaban kasa ba zai warke ya dawo gida ba. Kai jama’ah! Don Allah dubi irin wannan tatsuniya. Domin wannan karya da wannan mutum ya sharara, ai ko jahili murakkabi wallahi ba zai yarda da ita ba. Wai su me yasa irin wadannan mutanen ba su da abokanan adawa sai masu Martaba sarakuna. Ni ban san laifin da suka yi masu ba!
Irin matsalolin da muke fuskanta kenan a nan garin Okene, a inda wasu tsirarun matasa, masu zafin addini, wadanda suke kiran kan su cewa su Ahlis-Sunnah ne, alhali kuwa karya suke yi, su ba Ahlis-Sunnah ba ne. Domin Ahlis-Sunnah na gaskiya zaka same shi yana mai biyayya da nuna da’a ga shugabanni, akan abunda ba sabawa Allah ba ne da Manzon sa (SAW). Yaran nan sun sa Sarkin Okene (Ohinoyi of Ebiraland) a gaba da batanci da cin mutunci iri-iri. Saboda suna ganin kamar suna da goyon bayan gwamna Yahaya Bello. Kiri-kiri sun hana Sarkin ya nada limamin gari, bayan rasuwar liman na da, yau kusan shekara daya kenan. Sun ce su sam Sarki baya da ikon ya nada masu limami, na babban Masallacin Okene. Masallacin da ma mahaifin Sarkin ne ya gina shi, a lokacin da wadannan matasa watakila ba’a ma haife su ba. Gwamna yana kallon wannan al’amari amma yaki ce masu komai. Domin ko satin da ya wuce sai da wasu matasa suka yiwa Sarkin ihu, suka wulakanta shi a sallar juma’ah.
Duk wannan fa ‘yan uwa, yana faruwa ne saboda irin yadda gama-garin mutane suke ganin ‘yan siyasar nan suna wulakanta muna sarakuna masu daraja, sarakunan da ko-mun-ki-ko-mun-so suna da alaka da addinin mu da al’adun mu.
Yaku ‘yan uwa, a wannan lokaci da muke ciki, lallai akwai bukatar ‘yan siyasar nan indai har da gaske suke yi, suna kishin yankin su da talakawan su, to su jawo sarakunan nan, su nemi shiryawa da su, su nemi hadin kan su domin samun zaman lafiya da ci gaba mai dorewa a arewa. Domin duk dan siyasar da yake wulakantawa da raina Sarki, to lallai ba ya son ci gaban mutanen sa, kasancewar sarakuna suna da muhimmanci a cikin al’ummah.
Sannan mu kuma mabiya, talakawa, ya zama wajibi mu zamanto masu girmama sarakunan mu, da dukkanin hukumomin mu. Sannan ya zama dole a gare mu mu zama masu da’a da biyayya ga shugabanin mu, da jami’an tsaron mu, domin suna bukatar goyon bayan mu da addu’o’in mu dari-bisa-dari domin tunkarar wadannan fitintinu.
Yanzu don Allah mu dubi yadda ta’addacin Boko Haram yake neman ya sake yin kamari. Mu dubi yadda hanyar Damaturu zuwa Maiduguri ta ke nema ta koma tarkon mutuwa, wanda a kusan kullum sai ‘yan ta’addan na Boko Haram da ISWAP sun yi shigar sojoji, sun tare hanyar, sun kashe na kashewa sun yi garkuwa da wasu.
Mu dubi matsalar rashin tsaro a jihohin Kaduna, Katsina, Sokoto, Zamfara da sauran jihohin mu na arewa!
Yanzu idan har ba mu yi kokarin yin sulhu da juna ba, idan har manyan mu basu hada kawunan su ba, don Allah ta yaya zamu iya shawo kan wadannan matsaloli?
Yanzu don Allah ku dubi yadda abokan zaman mu, mutanen kudu-maso-yamma, wato yarbawa, suka hada kan su, suka kirkiro wata irin rundunar tsaro mai suna Amotekun, duk da cewa mun san wannan wani shiri ne na tunkarar 2023 suke yi! Amma mu ko hukumomin Hisba da ke da alaka da addinin mu, ‘yan siyasar da babu tsoron Allah tare da su sun siyasantar da su. Shin yanzu don Allah haka zamu zauna muna yakar juna, muna cin mutuncin juna, muna kokarin ganin bayan juna, alhali matasanmu na arewa, kullum suna ta yin tururuwa suna shiga cikin kungiyoyin ta’addanci daban-daban? Idan fa bamu shiga taitayin mu ba fa wallahi…
Ina rokon Allah ya kyauta, ya kawo muna mafita ta alkhairi, amin.
Dan uwan ku, Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuto daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa a lambar waya kamar haka: 08038289761.