Kungiya ta yi kira da a amince wa mata su rika saka gajerun ‘Siket’ a lokacin NYSC

0

Kungiyar daure wa mata Gindi su rika saka guntun Siket mai suna ‘Serve With Skirts Movement’ ta gudanar da zanga-zangar lumana da kira ga hukumar kula da dalibai masu aikin bautar kasa, NYSC da ta amincewa mata su rika saka gajerun siket a lokacin aikin yi wa kasa hidima

Shugaban kungiyar Udochi Emmanuel ta bayyana cewa duk shekara sai ma’aikata ko sojojin dake sansanin NYSC sun tozarta mace kan rashin saka wando a sansanin.

Udochi ta ce hakan da ake yi bai kamata ba saboda tauye wa masu haki ne ake yi bisa kamar yadda dokar kasar ta gindaya.

“Mun yi ta bibiya da kira ga hukumar NYSC ta amincewa duk dalibar da bata so saka wando ta rika saka siket amma hukumar ta toshe kunnuwar ta, ta yi mana kememe.

“Kada fa a manta mutanen da suka yi wa kasar nan hidima shekarun baya da suka gabata sun saka siket ba tare da kowa ya tilasta su ba.

“Mun fara tattaunawa da gwamnati kan saka siket tare da saura rigunan da ake sakawa na NYSC.

Udochi ta ce kungiyar za ta garzaya kotu idan har ba su samu biyan bukata ba.

Wannan kungiya ta gudanar da zanga -zanga ne bayan NYSC a jihar Ebonyi ta kori wasu mata biyu daga sansanin horo a dalilin rashin saka wando.

Wata dake cikin kungiyar Patience Noble ta bayyana cewa ita ma haka aka kore ta daga sansanin NYSC na jihar Ebonyi a dalilin rashin saka wando.

“Idan ni cikakkiyar ‘yar kasar nan ne bai kamata a tilasta ni kan irin kayan da zan saka ba a lokacin da nake wa kasa na hidima.

Bayan haka kakakin hukumar NYSC ta jihar Ebonyi Ngozi Ukwuoma ta bayana cewa NYSC ta kori wadannan mata biyu daga sansanin saboda kin saka wando sannan hakan ya biyo bayan wayar da su kan mahimmancin saka wando da yin biyayya ga dokokin NYSC da hukumar ta yi kokarin yi amma matan suka ki bi.

Idan ba a mata ba a watan Maris din 2018 ne majalisar wakilai ta yi watsi da gyara wasu bangarorin dokokin hukumar NYSC domin bari mata su fara saka siket.

Share.

game da Author