Ofishin Jakadancin Kasar Amurka da ke Iraqi ta umarci ‘yan kasar ta dake kasar Iraqi da su gaggauta ficewa daga kasar tunda wuri ba tare da wani jinkiri ba.
Hakan ya biyo bayan luguden bama-bamai ne da mayakan Amurka suka yi a tashar jirgin sama dake Iragi da ya kashe wani babban Janar din sojan kasar Iran Qasem Soleimani, da wani shugaban kungiyar Hezbollah da suke tare Abu Mahdi al-Muhandis.
Gwamnatin Amurka dai ta ba da sanarwar aikata haka a bisa umarnin shugaban kasa Donald Trump.
Wannan hari ya tada wa gwamnatin Iran hankali sannan kuma ta lashi takobi sai ta maida wa Amurka Martani. Ba za ta yi hakuri da wannan kisa da aka yi wa wadannan kwamandoji na ta ba.
Ita kanta gwamnatin Iraqi ta yi tir da wannan hari sannan kuma ko a can kasar Amurka din wasu da damu sun nuna rashin jin dadin su ga wannan hari da aka kai kasar Iraqi din.