Koyar da manyan harsunan Najeriya wani ginshiki ne na samar da fahimtar juna a tsakanin Al’ummomin Najeriya, Daga Anas Ɗansalma

0

Na san tambayar farko da za ta faɗo wa mai karatu ita ce……ta yaya koyar da harsunanmu na gida za su inganta zamantakewarmu?
Sadarwa (communication) wata hanya ce ta musayar saƙo a sakanin al’umma wacce muhimmin ginshiƙinta shi ne harshe (language) ko kuwa amfani da wasu hanyoyi na musamman domin isar da saƙon. Misali, ta amfani da ishara ko kwatanci (sign language) wanda masu larurar ji ke amfani da ita ko kuma rubutun makafi wanda suke yi da taimakon abubuwa na musamman.

Kamar yadda muka sani, Najeriya ƙasa ce mai ɗimbin jama’a da kuma dubunnan harsuna da ƙabilu mabambanta (diversity) wanda hakan ya haifar da matsaloli masu yawa tun bayan gushewar Turawan mulki. Irin waɗannan matsaloli sun haɗa da: rikice-rikice na addini da na ƙabilanci da kuma dangantakarwa (nepotism). Rayukan da suka salwanta kuwa, sun wuce ƙirgen yatsun hannu. Ga zaman ɗar-ɗar wanda al’umma wannan ƙasa ke fama da shi a lokutan zaɓuka na ƙasa da sauransu.

Haƙiƙa, irin waɗannan dalilai na da yawa da ke ƙara rura wutar irin waɗancan matsaloli musamman dalilai na siyasa da kuma ƙoƙarin ci-da-gumin-wani (exploitation). Ina ga, ƙari a kan waɗannan matsaloli shi ne na rashin samun fahimtar juna a tsakanin talakawan Najeriya da muke fama da shi saboda rahin fahimtar yarukan (languages) juna. Saboda muhimmancin harshe ne dai Allah ya sanya shi ɗaya daga cikin ni’imomin da ya yi wa ɗan’adam saboda godiya shi a kan dabbobi waɗanda suna ma ihunsu da kuma su ke isar da saƙonni masu yawan gaske a tsakaninsu.

Hakan ta sa ya sanya mu cikin ƙabila daban-daban da kuma hanyar isar da saƙo, shi ma kuma daban-daban a tsakaninmu. Wannan ita ce hanya ɗaya da za mu yi alfahari da juna ba rikici da kyama ko cin zarafin juna ba. Abin da talakawan Nijeriya suka gaza fahimta kenan!
Don haka, sadarwa wata hanya ce ta warware komai da komai wanda idan aka rasa taimakon harshe, to zai zama an gaza samun komai.

Addini ko bambance-bambancen al’adu ba ita ce matsalar Nijeriya ba. Matsalar Nijeriya shi ne ungulu da kan zabuwa da muke yi wajen ƙin karɓar gaskiya wanda hakan ya sanya addini da banbance-bambancen al’ada yin tasiri a tsakaninmu da har muke amfani da Turanci domin samar mana da haɗin-kai a tsakaninmu, inda kuma harsunanmu ke cigaba da kasancewa katangar rashin fahimta kuma a haka muke yaudarar kanmu da cewa kanmu a haɗe yake .

A zahiri, za mu samu haɗin kai ne a lokacin da muka yarda da yin maraba da kuma juriya ta cuɗanya a tsakaninmu. ‘Yan siyasar mu kyakkyawan misali na yadda suke mance duk wani bambanci tare da rabe albarkatun ƙasa cikin ruwan sanyi.

Bari In fara da yi mai karatu tambaya na haikaito kanka a wani yanayi na yaɗuwa da ɗan ƙabilar Yoruba ko Igbo ko Ibira sannan kuma ya tarar cewa ka iya yarensa ko da ba yawa, yaya kake jin zai yi maraba da kai? Sannan ya kake ji a lokacin da kake tsundum cikinsu ko su suke a cikin masu wani harshen? A wasu lokuta rashin fahimtar harshen juna kan sa mana zargin ko ana zaginmu ne ko kuma gulmarmu. Kuma sanin cewa wasu ba sa fahimtar mu kan sa wasunmu amfani da harshen wajen yin abin da bai da ce ba.

Idan ana batun Ingilishi, to a gaskiya a ɗabi’ance yana samu jin daban muke a maimakon a abu guda ɗaya domin yakan sa mu tuna cewa muna da namu harshen. Ingilishi na kawai samu ne a ɗauke mu a matsayin masu ilimi waɗanda muka je makaranta. Har ma idan mutum bai iya Turanci ba ko wani harshe na ƙetare, sai ka ga ana masa kallon jahili ko da kuwa zai iya ƙera jirgin sama ko yin wani abu na fasaha. Je ka unguwanninmu ka ga yara masu fasaha da kuma manya da ke da hikimar ƙirƙire-ƙirƙire, abin burgewa!

Iya harsunanmu na gida abu ne da zai cire mana rashin jin ɗarɗar a ko’ina za mu kasance ko a Enugu ga ɗan Arewa ko a Kano ga ɗan Enugu ko Bayelsa. Zai kuma sa mu amincewa da juna da kuma sauƙaƙa mana wajen kasuwanci. Wannan zai sa harshen da ya fi sauƙin koyo da fahimtuwa ya za ma harshen kasuwanci a ko’ina a faɗin ƙasar. Ka ga cigaba ya samu tushe!

Saidai yana da kyau mu lura cewa, Turanci (Ingilishi) ba zai zama jujin zubarwa ba domin kuwa ya riga ya sama wa kansa gindin zama (kamar yadda nake fatan harsunanmu su samu) a ƙasashe da yawa na duniya kuma a halin da ake ciki iya shi wajibi ne. Amma mai zai hana mu yi tsari na saka irin waɗannan harsuna a matsayin “harasan ƙetare” tare da ɗaukar su a matsayin “subject,” wani darasi na daban. Akwai Arabiyya da Faransanci da Sunanci da ma wasu da dama da ke ƙoƙarin yin kutse gare mu, kuma In ban da Arabiyya, babu wanda ba baraza ba ne ga al’adar mu, musamman mu Hausawa.

Cigaba da koyar da su a matsayin ginshiƙin komai namu, zai sanya masu tasowa ne yi wa harsunansu kallon biyu sha tara da kallon su a matsayin kayan al’ada na da tare da jin gwanancewa wajen baƙin harsuna shi ne zamananci kuma rashin iya su rashin wayewa ne. Dubi yaran mu na zamani, ka tambaye su mene ne “Laulawa ko mummuƙi ko ma tsumma?” Sai ka ga sun zuba ma na mijinta. Sam, wannan ba burgewa ba ce ko ace ai yara ne sai gaba da iya!

A ranar 21 ga watan Nuwamba, 1961 a zauran Majalisar Waƙilai ta Nijeriya an tafka muhawara wajen ganin an yi amfani da Hausa a matsayin harshen ƙasa, amma sai aka samu tsoro na cewa Hausa za ta danne sauran ƙabilu kenan, wanda cecekuce ya haifar da tsayar da wannan yunƙuri.

A ra’ayina, wannan batuna ba irin wannan ba ne. Batuna shi ne na ganin han sanya fahimta ta manyan yarukan Najeriya a tsakanin al’umma wanda hakan na nufin kowa da harshensa, amma babu ƙyamar juna.

Ai ko su Turawan da suka shigo, domin su samu karɓuwarmu, ai dagewa suka yi da koyon harsunanmu da al’adunmu. Da yake suna da manufa ta juyar da ƙwaƙwalenmu sai suka shiga koya mana harshensu don koyon da iya harshen mutum na sa wa ka so shi. Don haka, idan dai har ‘ya‘yanmu na kan cigaba da fafutukar iya harshen Ingilishi, a inda kuma muke shigo musu da harshen Faransanci, to mai zai hana mu koya mu su namu?

Me zai samu ɗanka Bahaushe don ya iya Iyamuranci ko kuma shi mai zai samu ɗansa idan ya iya Hausa? Ko kuwa muna tsoron ba za su iya haɗa koyon Ingilishi da faransanci da muke ƙaƙaba musu ba a yayin koyon Hausa da Yarabanci da Iyamuranci? Amma idan muna jin tsoro ne, ta yaya yaron da ya iya Faransanci koyon biyu daga cikin harsunan ƙasarsa zai zame masa jidali? Bari in mana tuni, bincike ya nuna cewa yara a farkon shekarunsu na rayuwa na iya harsuna kusan goma. Kuma ƙwaƙwalensu tamkar mayen ƙarfe ne wajen wawason abin da ake koya musu da riƙe shi. Wannan ba zai zama matsala ba, matuƙar akwai tsarin koyarwa mai nagarta da mu’amala mai kyau a tsakanin malamai da ɗalibai.

A ƙarshe, domin samun nasarar wannan abu, akwai buƙatar ma’aikatar ilimi ta yi sabon tsari na koyar da harsunan gida tare da koyar da yara duk darussa daga aji ɗaya zuwa uku a makarantun firamare da harshen uwa. Sannan kuma a sakandire sai a fara wannan tsari na koyar da su harsunan gaba ɗaya ga yara.

Iya na da nasu rawa mai muhimmanci wajen cigaba da yara wa yara harsunansu a yayin da suke gida ko da kuwa ta hanyar zama mafassara ne wajen haɗe musu abin da abu kaza ke nufi a wannan harshe da kuma ɗaya ko sauran harsuna. Amma harshen uwa da na gida ya zama madogara ga fahimtarsu. Malaman Jami’o’i da sauran al’umma su ne za su dage wajen rubuce-rubuce da kuma jan hankalin ɗalibai kan muhimmancin harsunan gida. Haka kuma kamata ya yi kowacce jami’a daga ƙasar nan sanya darasin bai-ɗaya (GSP) kan harsunan gida kamar yadda ake wa harshen Ingilishi. Yan kasuwa ma su riƙa dagewa wajen jimmintan abokan kasuwancinsu da harsuna daban-daban tare da amfani da su arubuce-rubuce na talluka da kuma ofisoshinsu a kanfanunuwa.

Yana da kyau a riƙa tuntuɓar masana harsunan domin gudun kuskure. Da haka sai a samu ɗa mai ido biyu domin ka da ayi abin da marigayi ɗan masanin Kano ke cewa a wani bidiyonsu kan “duk al’ummar da ke kwaikwayon wata al’ummar ta fuskar al’ada, to za ta zama naƙasashen kwafin wancen al’adar ne, don haka za a rasa ta a gida kuma a wajen ƙetaren sauran al’ummun babu ita sam.” Wato ɓatan-bakatantan kenan! Ba wan, ba ƙanin, karatun ɗan-kama.

Tambayar dai a ƙarshe ita ce, shin a shirye muke wajen ganin mun koyi sauranhar sunanmu na gida Nijeriya, musamman manyan nan guda uku?

Daga Anas Ɗansalma
dansalma35@gmail.com

Share.

game da Author