KOTUN KOLI: Za a yanke hukuncin zaben Kano ranar 20 Ga Janairu

0

Cif Jojin Najeriya, Babban Mai Shari’a Tanko Muhammad ya bayyana cewa za a yanke shari’ar zaben gwamnan Kano a ranar 20 Ga Janairu, 2020.

Hakan ya biyo bayan dogon lokacin da lauyoyin mai kara Abba Yusuf da na wanda ake kara, Abdullahi Ganduje da INEC suka dauka ana tabka mahawara a gaban alkalan Kotun Koli su bakwai.

Alkalai 7 ne dai ke zaman sauraren kararrakin gwamnonin da ake sa ran yanke hukunci daga yau Talata.

Babban Mai Shari’a Mohammed Tanko, kuma Cif Joji na Najeriya, shi ke shugabantar alkalai 6, sais hi cikon na 7 din.

Kano: Tsakanin Abba Gida-gida da Ganduje

Tun da farkon kafsawa dai lauyan Abba Yusuf Adegboyega Awomolo ya bayyana a rubuce cewa ya na so kotu ta bada umarnin a ci gaba da sauraren yanke hukuncin wannan kara.

Kuma ya na rokon kotu ta dubi rashin adalcin da aka yi wa wanda ya ke karewa, wato Abba na jam’iyyar PDP, sannan ta kwato masa hakkin sa daga hannun Gwamna Abdullahi Ganduje da kuma jam’iyyar APC.

Awomolo ya yi tsokacin cewa mai bayyana sakamakon zabe da shugaban tattatara sakamakon zabe ya soke zaben rumfuna 207, ya ce wai zabe bai kammalu a wuraren ba, daga nan ya sa wata ranar 23 Ga Maris, 2019, aka sake zabe.

Daga nan ya ce soke zaben da aka yi bayan da aka rigaya aka bayyana sakamakon zabe, rinto ne, giriftu ne, kuma shugaban zaben ba shi da ikon yin haka a dokar kasa.

Wannan babban lauyan na Abba Yusuf ya ce, “sakamakon zaben 23 Ga Maris, wanda aka ce shi ne zaben ‘inconclusive’ na rumfuna 207, haramtacce ne.”

“Halastaccen zabe shi ne wanda aka na gwamnan Kano, kuma shi shugaban zaben na Kano ya sanar da sakamako a ranar 11 Ga Maris, 2019.

“A karshe ina rokon masu girma alkalan Kotun Koli su dubi wannan dawurwurar zabe da aka yi a Jihar Kano, su amince cewa zaben da aka yi ranar 9 Ga Maris, shi ne sahihin zabe, kamar yadda Sashe na 179 (2) a da ya tanadar.

Sai dai shi kuma lauyan INEC, Ahmed Raji ya roki Kotun Koli ta yi fatali da rokon da lauyan Abba Yusuf ya yi.

Ya ce ba a soke kuri’u ko zabe ba.

Lauyan APC kuma lauyan Ganduje, Duru ya ce sun rigaya sun bayyana matsayin su a gabatarwar da ya rigaya ya yi.

Shi ma ya kawo hujjojin sa da ke nuna cewa lauyan Abba bai gabatar da sakamakon mazabu 207 ba, ballantana har ya ce zaben 9 Ga Maris, 2019 ya kammalu.

Ya ce sannan kuma akwai rumfuna har 62 da ba a harhada sakamakon su ba zaben 9 Ga Mayu.

Shi ma lauyan APC, Alex Iziyion roko ya yi Kotun Koli ta kori karar da Abba Yusuf ya kai.

Mai Shari’a Tanko Mohammed dai ya ce a ranar 20 Ga Janairu, 2020 za a yanke hukunci.

Daga nan kuma sai kotu ta tafi hutu na dan takaitaccen lokaci.

Share.

game da Author