Kotun koli dake Abuja ta tsige gwamnan jihar Imo, Emeka Ihedioha na jam’iyyar PDP, ta umarci hukumar Zabe ta nada Hope Uzodinma na jam’iyyar APC.
Alkalai 7 duka sun amince da wannan hukunci wadda babban Mai sharia Muhammad Tanko ya karanta.
Shi dai Hope ya zo na hudu ne a zaben gwamnan jihar Imo.
Discussion about this post