Gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed, ya bayyana cewa ya yi matukar bakin ciki dangane da yadda Kotun Koli ta yi juyin-waina da tsohon gwamnan jihar Imo, Emeka Ihedioha na PDP, ta maye gurbin sa da Hope Uzodinma na APC wanda ya zo na hudu a zabe.
Bala ya ce abin da Kotun Koli ya yi wa Ihedioha zai iya faruwa da shi, ko ma sauran gwamnonin da aka yanke wa hukunci a Kotun Koli.
Da ya ke jawabi a wurin taron walimar taya shi murnar yin nasara a Kotun Koli, Gwamna Bala ya yi bayanin cewa shi kan sa tsohon gwamnan Bauchi Mohammed Abubakar ya san bai ci zabe ba.
Kuma ya san cewa shi Gwamna Bala din ya san Abubakar bai ci zabe ba, amma duk da haka ya bata lokacin sa, kuma ya bata lokacin gwamnan ya garzaya kotu neman hakkin da ba na sa ba.
Daga nan sai Bala ya nuna rashin jin dadin yadda Kotun Koli ta tsige Ihedioha, wanda ya kira abokin sa kuma aminin sa, sannan kuma wanda suke jam’iyya daya PDP.
Ya ce ji da ganin yadda Kotun Koli ta yi juyin-waina da Ihedioha, sai ya raya a zuciyar sa cewa shi ma za a iya yi masa irin wannan juyin-wainar.
Amma da ya kara fawwala komai ga Allah, kamar yadda ya bayyana, sai bai karaya ba, domin ya na ji a jikin sa nasara a kan sa ta ke, tunda dai ya na da yakini, tabbataci da kuma hujjojin cewa shi ne ya yi nasara.
Da ya koma kan tsohon gwamna Abubakar na Bauchi, Gwamna Bala ya ce shi aikin da ke gaban sa zai maida hankali a kai, ba zai tsaya bincikar sa ba.
“Amma fa idan cikin aiki nan a ci karo da wani wuri ko wasu wuraren da ake ganin tsohon gwamnan ya yi burum-burum, to zan bincike shi.
“Domin ni ma da na bar Ministan Abuja, babu irin binciken da ba a yi min ba. Amma a karshe ba a samu wani asusu ko da guda daya tal da na boye kudade ba.
“Babu wanda aka fi bincike bayan ya sauka daga mulki a kasar nan kamar ni.” Inji Gwamna Bala Mohammed.