Kotu ta tsare shugaban makarantar da ya rika yin lalata da tagwayen daliban sa

0

Kotun dake Ikeja jihar Legas ta kama wani shugaban makarantar sakandaren ‘Legati College’ mai suna Samson Adeyemo da laifin yin lalata da wasu tagwaye mata.

A zaman da kotun ta yi ranar Litini Adeyemo mai shekaru 41 dake zama a lamba ta 8 hanyar Odesanya, Abule ya amsa laifin sa cewa ya yi lalata da wadannan tagwayen mata.

Adeyemo ya ce ya fara haduwa da daya daga cikin tagwayen ne a 2016 amma bai fara lalata da ita ba sai a 2017.

“ A wannan lokaci na yi soyayya da wannan yarinya inda har na yi mata ciki.

“ Na so in aureta saboda ina son ta amma iyayenta suka ki amincewa da soyayyata suka zubar da cikin da take ke dauke da shi,suka sa na biya su Naira 200,000 sannan suka truro min wasu ‘yan iska har gida suka yi mini shegen duka.

” Daga baya sai ‘yar uwarta ta garzayo wuri na da kanta cewa wai ta na so na mu yi soyayya da juna. A Yanzu dai muna tare da wacce nake so sannan muna wannan zama ne da izinin iyayenta.

Bayanai sun nuna cewa Adeyemo a cikin ofishinsa ne yake lalata da wadannan tagwaye sannan ya musanta yin lalata da sauran dalibai makarantar sa.

Sakamakon binciken asibitin Mirabel Centa ya nuna cewa Adeyemo ya dade yana lalata da wadannan tagwaye.

Alkalin kotun Sherifat Solebo ta dage shari’ar zuwa ranar 24 ga watan Fabrairu.

Share.

game da Author