Kotu ta daure Runsewe, ta Umarci Sufeto Janar ya kamo shi

0

Kotun Babban Birnin Tarayya, Abuja ta kama Shugaban Hukumar Al’adu ta Kasa Olusegun Runsewe da laifin dauri, saboda kin bin umarnin kotu da ya yi.

Mai Shari’a Jude Okeke, wanda ya bada umarnin a kulle Runsewe a kurkuku yau Alhamis, yace “a garzaya da shi kurkukun Kuje har sai ya saduda, ya nabba’a, ya daina yi wa kotu galatsi.”

Sannan kuma Mai Shari’a Okeke ya umarci Sufeto Janar na ’yan sanda cewa duk inda Runsewe ya ke, a kama shi, a garkame shi a kurkuku.

Mai Shari’a ya ce wannan umarni zai zama gargadi ne da kuma darasi ga duk wani ma’aikacin da zai rika bijire wa umarnin kotu, ko kuma raina kotu.

Okeke ya ce abin da Runsewe ya yi wa kotu cin fuska ne da kuma raini.

Mai Shari’a Okeke ya ce umarnin a daure Runsewe ya taso ne daga wata kara da kamfanin Ummakalif Ltd ya shigar.

An dai kai karar Runsewe a matsayin san a Darakta Janar na NCAC da kuma Ministan Babban Birnin Tarayya, sai Ministan Al’adu da Bude-ido.
An maka su kotu ne saboda garkame Kauyen Yada Al’adu da Sassake-sassake na cikin Abuja da aka yi.

Wannan karimtsa dai ta samo asali ne tun a ranar 21 Ga Yuni, 2019 da aka shigar da kara Babbar Kotun Abuja.

Mai kara ya nemi kotu ta kulle Runsewe a kurkuku saboda ya ki bin umarnin kotu da ta bayar tun a ranar 15 Ga Disamba, 2019.

Tun farko dai Mai Shari’a Salisu Umar ne a ragargaji Hukumar NCAC wadda Runsewe ke shugaban ta a cikin wani hukunci da yanke a ranar 6 Ga Maris, 2018.

Mai Shari’a Salisu ya ce hukumar ta ki darakta kotu, inda duk da cewa kotu ta ce kada a garkame wurin, amma sai da aka garkame shi.

To cikin 2018 sai likkafar Umar ta yi gaba zuwa Kotun Daukaka Kara, inda aka maida shari’ar a hannun alkali Okeke.

Sunan Runsewe ya kara kaurin suna bayan da PREMIUM TIMES ta buga labarin wata harkalla da aka danganta ofishin sa da aikatawa.
Sai dai kuma ya yi raddin cewa ba a karkashin sa aka bada kwangilar ba.

Ya ce an bada kwangilar tun lokacin wanda ya gada na kan shugabancin hukumar, watau kafin shi Runsewe din ya zama shugaba.

Yanzu dai ta rage a ga shin ko Sufeto Janar na ‘Yan Sanda Muhammad Adamu shi ma zai bin umarnin kotun ya sa a kamo Runsewe a kulle a kurkukun Kuje?

Ko kuwa shi din ma kamar Runsewe, bijire wa umarnin kotun zai yi?

Share.

game da Author