Ko kai waye, Ko maihaifin ka waye, Idan ka taba handamar kudin Adamawa, Za ka kuka da kan ka – Fintiri

0

Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri ya bayyana cewa gwamnatin sa za ta bincike duk wanda da ya taba aiki a jihar tun daga jiha zuwa kananan hukumomin kuma ya handame kudin gwamnati ko shi wanene kuwa.

” Ina son in sanar muku cewa gwamnati na za ta bincike duk wani da ya taba aiki da gwamnatin jiha ko na kananan hukumomin jihar, kuma ya wawushe kudaden gwamnati ko shi waye kuma ko waye mahaifin sa a jihar.

Gwamna fintiri ya yi wannan gargadi ne a lokacin da yake jawabi ga magoya bayan jam’iyyar PDP bayan nasara da suka yi a kotun koli.

Ya tabbatar wa ‘ya’yan jam’iyyar cewa gwamnatin sa gwamnatin samar wa jihar Adamawa ci gaba ne da kuma farfado da jihar daga yadda kuncin da gwamnatocin baya suka saka ta a ciki a baya.

Ya kara da cewa zai binciki asusun gwamnatin jihar falle-falle, sannan ya gangara zuwa na kananan hukumomi ya bude takardun su suma dalla-dalla domin zakulo wadanda suka yi wa jihar tabo ta ko ina.

Share.

game da Author