Real Madrid ta doke babbar abokiyar adawar-cikin-gidan ta, Atletico Madrid, a wasan karshe na Supercopa da ci 4:1 a bugun daga kai sai mai tsaron gida.
An yi wasan na karshe a babban filin Sarki Abdallah na Saudiyya da ke Riyadh, babban birnin kasar.
Dama kuma a can din ne Madrid ta doke Valencia mai rike da kofi a wasan kusa da na karshe da ci 3:1.
Sannan a filin wasan ne dai Atletico Madrid ta doke Barcelona a wasan karshe da ci 2:1.
A wasan tsakanin Madrid da Atletico da aka kafsa ranar Lahadi da dare, an tashi minti 120 canjaras, wanda hakan ya kai ga bugun daga kai sai mai tsaron gida.
’Yan wasan Madrid, Rodrygo, Dani Carvahal, Luca Modric da Sergio Ramos duk sun ci kwallayen su. Yayin da Saul Niguez da Thomas Parte na Atletico suka baras da na su bugun.
Wasan ya yi zafi sosai, musamman daf da tashi, inda dan wasan Madrid Fede Valverde ya kayar da dan wasan Atletico, Morata, wanda ake ganin da ba a kayar da shi ba, to zai iya cin kwallon.
Tuni dai mai horas da ‘yan wasan Atletico, Diego Simone ya bayyana cewa ya yi mamakin yadda aka bai wa Velverde gwarzon dan wasan, bayan an rigaya an ba shi jan katin kayen da ya yi wa Morata.
Kuma ya ce Velverde ya zalinci Atletico, ya hana su daukar kofi.
A yanzu dai mai horas da Madrid Zidane ya ci kofi 10 kenan a matsayin sa na mai horas da kulob din.
Velverde dai daga baya ya bai wa Morata hakuri. Shi kuma Zidane ya jinjina wa Velverde, ya ce komai kenan dai, ‘wai bukatar maje-Haji sallah!”