KISAN SOLEIMANI: Majalisar Kolin Musulunci ta gargadi matasan Najeriya su guji zanga-zanga

0

Majalisar Koli ta Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA), ta yi kira ga matasa Musulmi na kasar nan cewa su kai zuciya nesa, kada su gudanar da zanga-zanga dangane da kisan Kwamandan Sojojin Iran, Qassem Soleimani da Amurka ta yi.

Cikin wata sanarwa da Shugaban Yada Labarai na NSCIA ya fitar a Abuja, Ibrahim Aselemi ya ce NSCIA ta na rokon matasan kasar nan kada su bari barin rai ya kai su ga tada tarzoma, su jure, domin tabbatar da zaman lafiya.

Majalisar ta ce bambanci ko rikicin da ke tsakanin Iran da Amurka, ta hanyar zama taburin sulhu da lalama ce kawai za a iya warware shi.

“An jawo hankalin NSCIA cewa wasu matasa na shirin gudanar da zanga-zangar lumana domin nuna rashin jin dadin su kan kisan babban kwamandan Iran, Janar Qassem Soleimani a Iraqi.

“Duk da cewa wannan zanga-zanga ta lumana da suka yi shirin gudanarwa na daya daga cikin turbar da dimokradiyya ta shimfida, duk dai da haka NSCIA na ganin cewa bai kamata a gudanar da zanga-zangar a daidai wannan mawuyacin lokaci da mu ke ciki ba.”

Kisan Soleimani ya jawo fushin milyoyin jama’a, musamman matasa a kasashen musulmin duniya.

Bakin Hadari, Fito ta Gabas!
A yanzu haka bakin hadari ya tirnike duniya, wanda ake ta kaffa-kaffa kada ya rikide ya zama Yakin Duniya na 3, sanadiyyar kisan Soleimani da Amurka ta yi.

Bisa la’akari da rahotannin da manyan jaridun nan na Ingila, Daily Mail da kuma Daily Mirror, za a iya cewa Iran ta fusata, ta kekketa takardar kulla yarjejeniyar lallamin ta na ta dakatar da binciken kera makaman nukiliya.

An kulla wannan yarjejeniya cikin 2015.

Amma yanzu Shugaban Kasa Hasan Rouhani ya fitar da sanarwar ci gaba da aikin nukiliya da kuma tara sinadaran yuraniyan, wadanda ake hada nukiliya da su.

Dan Majalisa Abolfazi Abuturabi ya bayyana cewa Irann za ta iya kai hari har cikin Fadar White House, fadar Shugaban Amurka Donald Trump.

Wanda ya shirya gangamin taron jana’izar Soleimani, ya yi kiran kowane Ba’Irane ya bada gudummawar dala milyan daya, domin a tara dala milyan 80, wadda za a bai wa duk wanda ya kashe Donald Trump murus.

Majalisar Kasar Iraqi kuma a zaman ta na jiya Lahadi ta kada kuri’ar amincewa da korar sojojin Amurka 5,000 da ke cikin kasar.

Amurka na ci gaba da nausawa da sojojin ta da ke Airborne Division na 82 zuwa cikin Gabas Ta Tsakiya.

Daukacin Mambobin Majalisar Iran sun rika rera wakokin tsinuwa ga Amurka da Isra’ila, a zaman da ta yi jiya Lahadi.
An yi jana’izar Janar Soleimani a Babban Masallacin Jamkaran, da ke tsakiyar birnin Ahvez.

An yi ittifakin ba a taba ganin taron dimbin jama’a a wurin jana’iza a duniya ba, kamar jana’izar Soleimani.

Babban Kwamandan Dakarun Juyin Turu, wato Iran Revolutionary Guard, Janar Hosseini Salami, yace Iran za ta yi wa Amurka barnar da idan ta fice daga Gabas ta Tsakiya, ba za ta sake sha’awar turon sojojin ta ba, har abada.

Sanata Richard Black na Amurka, wanda tsohon sojan ruwan kasar mai ritaya ne, ya ce kisan Qassem Soleimani ya tabbatar da a yanzu Amurka ce ‘yar ta’adda, ba wai mai yaki da ta’addanci ba.

Jagoran Musulunci na Iran Ayatollah Khameini, ya shaida wa babbar ‘yar Qassem Soleimani cewa Iran za ta rama zubar da jinin da aka yi wa mahaifin ta.

Ya ce za su rama wa Iran da iyalan Qassem kisan da aka yi masa.

Share.

game da Author