Tun bayan da sojojin Amurka suka kashe Qassem Soleimani, daya daga cikin manyan kwamandojin Iran a cikin kasar Iraqi, abubuwa muhimmai sun faru a duniya a cikin kwanaki 3.
Ga kadan daga cikin abubuwan da suka faru:
1. Iran ta sha alwashin yin ramuwar-gayya a kan kasar Amurka. Ta ce sai ta rama fiye da abin da aka aikata mata.
2. Iran ta yi ikirarin ware wadansu wurare 35 na Amurka da za ta kai wa mummunan hari.
3. Amurka ta bada umarnin dukkan ‘yan kasar ta da ke cikin Iraqi su gaggauta ficewa daga kasar.
4. Shugaban Amurka Donald Trump ya ce idan Iran ta kai hari a wani wurin Amurka, za ta dandana kudar sabbin makaman kai hari na Amurka.
5. Rasha ta yi Allah-wadai da Amurka, ta ce kisan Qassem Soleimani da ta yi babban laifi ne.
6. Kungiyar Hada Kai ta Sojojin Tarayyar Turai, NATO sun bayyana ficewa daga kasar Iraqi.
7. Kawunan Mambobin Majalisar Amurka ya rabu biyu. Da masu goyon bayan Trump, wanda ya bada umarnin a yi kisan, da muka wadanda ke yin tir da aika-aikar da suka ce Trump ya aikata.
8. Farashin danyen man fetur ya karu a duniya, tsoron idan yaki ya barke a Gaban ta Tsakiya, danyen fetur zai yi karanci, musamman domin yakin kan iya shafar danyen man da Iran, Saudiyya da Kuwait ke hakowa.
9. Iran ta dora dakarun ta cikin shirin yaki da shirin ko-ta-kwana.
10. Isra’ila ta dora wasu mayakan kai hare-hare ta sama cikin shirin yaki, kasancewa abin da ya ci Doma, ba zai bar garin Awai ba.
Discussion about this post