Kisan Dan Jarida: Rundunar ‘yan sanda sun kama mutane biyu a jihar Adamawa

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta kama wasu mutane biyu da take zargin su kashe ma’aikacin jarida mai suna Maxwell Nashon.

Kwamishinan ‘yan sanda Audu Madaki ya sanar da haka da yake tattaunawa da shugaban kungiyar manema labarai ta kasa (NUJ) Chris Isuguzo a garin Yola.

Madaki yace sun kama wadannan mutane ne bayan kwanaki Shida da kashe Nashon.

“ Wadannan mutane na tsare a ofishin mu kuma suna taimaka wa jami’an tsaro da bayanan da za su taimaka wajen kama duk wadanda ke da hannu a kisar.

“ Rundunar za ta kamo duk wadanda ke da hannu a aikata wannan mumunar aiki domin a hukuntasu bisa ga doka.

Bayan haka shugaban kungiyar NUJ Isuguzo ya yabawa kokarin da ‘yan sandan suka yi wajen ganin sun cafko wadanda suka kashe ma’aikacin.

Ya yi kira ga manema labarai da jami’an tsaro da su hada kai musamman wajen ganin an samu zaman lafiya a kasar nan.

Maxwell Nashon ya yi aiki da gida radiyon dake Yola.

Rahotanni sun bayyana cewa masu garkuwa da mutane ne suka yi garkuwa da shi inda bayan ‘yan kwanaki suka kashe shi.

Share.

game da Author