Matasan yankin Keimoes da Upington da ke Gundumar Cape Town a Afrika ta Kudu sun bai wa ‘yan Najeriya awa 12 su fice daga yankin ko kuma jikin su ya gaya musu.
Shugaban ‘Yan Najeriya Mazauna Afrika ta Kudu, Adetola Olubajo, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai, NAN cewa ba ‘yan Najeriya kadai aka kora ba, har da ma wasu ‘yan sauran kasashe daban.
Da ya ke jawabi yau a Lagos, ya ce wani al’amari ne mai ban-takaici inda wani dan Najeriya ne mutumin Jihar Abakaliki ya burma wa dan sandan Afrika wuka da asubahin ranar Laraba, daga wata ‘yar tankiya.
Kisan dan sandan mai suna Nico Visagie da dan Najeriya ya yi ya harzuka al’ummar yankin.
Olubado ya ce har yanzu dai ba a san takamaman dalilin burma masa wuka da dan Najeriya ya yi ba, domin wanda zai iya bada shaidar abin da ya faru, shi ma an caccaka masa wuka, kuma yanzu haka ya na asibiti mutu-kwakwai-rai-kwakwai.
“Bayan faruwar wannan mummunan al’amarin sai al’ummar yankin suka fusata, suka rika banka wa dukiyoyin ‘yan Najeriya wuta.
“An kai wa ‘yan Najeriya hari a Upington, inda ba ma a can aka yi kisan ba. Sannan kuma aka kore su daga garin.
“Amma kuma kwakkwaran matakin da ‘yan sanda suka dauka a yau Alhamis ya kwantarcda hargitsin, sai dai fa har yanzu komai na iya faruwa.
Jami’an tsaro dai sun kama wasu da suka banka wa dukiyar ’yan Najeriya wuta.
“Tuni har an gurfanar da su a kotu a safiyar yau Alhamis, an kuma maganar beli.” Inji.
Daga nan ya tabbatar da cewa wanda ya kashe dan sandan ya na hannun jami’an tsaro, kuma za grfanar da shi kotu ranar Litinin mai zuwa.