KATUTUN RASHAWA: Mizanin da Kungiyar TI ta dora Najeriya duk karya ce -Gwamnati

0

Ministan Shari’a Abubakar Malami da kuma Hukumar EFCC, sun maida wa Kungiyar Transparency International martani bayan da kungiyar ta bayyana Najeriya a sahun farko na kasashen da rashawa ta yi katutu a gwamnatin su, a cikin 2019.

Jadawalin lalatattun kasashen da rashawa ta yi katutu dai ya nuna cewa Najeriya ce 146 a cikin kasashe 180, idan ana magana kan yaki da rashawa da cin hanci.

Najeriya ta koma ta 146 ne daga mataki na 144 da ta ke kafin 2019, wanda haka bai wa gwamnatin tarayya dadi ba ko kadan.

A makin da TI ta bai wa Najeriya wajen yaki da cin hanci da rashawa, kasar nan ta samu maki 26 bisa 100 na awon gejin shekarar 2019.

Wannan rahoto ya nuna Najeriya ba a samu ci gaba wajen yaki da cin rashawa a shekarar 2019 ba, sai ma rami aka kara ruftawa gaba biyu, daga matakin da kasar ta ken a 2018.

Sai dai kuma Ministan Shari’a Malami ya ce rahoton na TI ba abin dogaro ba ne, saboda babu wata hujjar da za a iya dogaro da ita.

Da ya ke hira a gidan talbijin na Channels a ranar Alhamis, Malami ya bayyana cewa irin nasarorin da wannan gwamnatin ta samu ba su yi daidai da karairayin da TI ta kantar aba. Sannan kuma ya ce kirdado ne kawai kungiyar ta yi, ba ta gabatar da wasu gamsassun hujjoji ba.

“Mu na iyakar kokarin mu sosai wajen yaki da cin hanci da rashawa, kuma za mu ci gaba da karin kaimi sosai, ba tare da yin la’akari da irin mataki, mizani ko ma’aunin da kungiyar TI za ta auna irin kokarin da muke yi ba.

Daga nan sai Malami ya kalubalanci TI ta fito da sahihan alkaluman da ta yi amfani da su har ta dora korarin da Najeriya ke yi wajen yaki da rashawa a sahun baya, kuma ta dora Najeriya a sahun farko na kasashe maciya rashawa a duniya.

Ita ma Hukumar EFCC, wadda ita ce hukumar da ke aikin yaki da cin hanci da rashawa, ta yi watsi da rahoton da TI ta fitar, ta na mai cewa shirme ne, kuma ba shi da tushe, sannan kuma abin takaici ne.

EFCC ta ce ba za ta bari wata kungiya ta karkatar da ita ba, wajen auna kokarin da ta ke yi da ma’auni na karya, rashin adalci da son rai ba.

Jam’iyyar PDP dai ta ce ba wani abin mamaki ba ne don an dora Najeriya a sahun farko na kasashen da rashawa ta yi wa katutu.

PDP ta ce irin yadda gwamnatin Buhari ke tafiya, an dora a daidai matakin da ya kamaci gwamnatin APC.

Share.

game da Author