A dalilin kashe sojojin kasar Nijar da Boko Haram suka yi a yankin kudancin kasar, cikin fushi shugaban kasar Momoudu ya fatattaki babban hafsan sojojin kasar sannan ya hada da sakataren tsaro da kwamandan sojojin kasa na kasar.
Mahara da ke da alaka da kungiyar Boko Haram da IPSWA sun bude wuta a hare-hare da suke kaiwa a wasu sassan kasar Nijar da Burkina Faso.
Akalla sojoji 71 ne suka aika lahira a tsakanin 10 da 25 ga watan Disamba baya ga mutane sama da 160 da suka karkashe.
Bayan haka kuma shugaba Momoudou sai ya garzaya kai tsaye zuwa kasar Faransa domin ganawar gaggawa da gwamnatin Kasar game da tsaro a kasar sa.
Sai dai kuma suma maharan sun dandana kudar su domin dakarun Nijar din sun kashe akalla mahara sama da 80.
Discussion about this post