Jam’iyyar PDP ta ragargaji Shugaba Muhammadu Buhari a kan furucin da ya yi cewa ba zai nada ‘halifan’ da zai tsaya wa APC takara a lokacin zaben 2023 ba.
Ranar Litinin ne Fadar Shugaban Kasa ta maida wa Tunde Bakare raddi cewa Shugaba Muhammadu Buhari ba zai fidda wani dan takara daya ya ce shi ne zai gaji kujerar sa a zaben shugaban kasa na 2023 ba.
Kakakin Yada Labarai na Buhari, Femi Adesina ya ce duk da Buhari zai so a zuciyar sa a ce ga wanda zai gaje shi, “to ba zai fidda wani ya ce shi zai zama ‘halifan sa’ ba.”
PREMIUM TIMES ta buga labarin da Tunde Bakare ya shawarci ya shawarci Buhari ya fito da wanda ya ke so ya gaje shi a zaben shugaban kasa na 2023 da APC za ta tsaida takara, idan lokacin ya zo.
Bakare ya ce shugabannin kasashe irin su China, Singapore da Afrika ta Kudu duk su na fidda wanda zai gaje su tun kafin su kammala wa’adin su a kan mulki.
“Mu koyi darasi daga Nelson Mandela, wanda kafin ya sauka daga wa’adin zango daya, sai da ya tsaida Thabo Mbeki da Cyril Ramaphosa.”
Sai dai kuma PDP ta fitar da sanarwa cewa Buharin ya gaza da ya kasa fito da wanda zai tsaya wa APC takara tun kafinn ya sauka daga mulki.
Kakakin yada labarai na PDP, Kola Olagbondiyan ne ya fitar da sanarwar, a madadin uwar jamiyya mai adawa, PDP.
PDP ta ce fara ka-ce-na-ce din batun wanda zai gaji Buhari tun yanzu, kafin ma a cika shekara daya da shiga zango na biyu, ya nuna cewa Buhari ya kasa ga gudanar da al’amurran shugabancin kasar nan.
Sannan kuma fargabar da Buhari ya nuna cewa APC na iya narkewa a bayan kammala mulkin sa, shi ma alama ce mai tabbatar wa al’ummar kasar nan cewa su sani fa APC ba abin dogaro ba ce.
“PDP na neman Fadar Shugaban Kasa ta bai wa ‘yan Najeriya hakuri dangane da kasassabar furta kalmar ‘danka mulki’ da ta yi amfani da shi wajen bayyana cewa ‘Buhari ba zai damka mulki’ ba ga….’
Ta ce furta hakan cin fuska ne da kuma rainin wayau aka yi wa al’ummar kasar nan, watau har Fadar Buhari ta nuna wa duniya cewa APC ce za ta mika mulki ga APC a 2023 kenan.
Daga nan sai ta ja hankain fadar shugaban kasa ta daina mafarkin cewa za ta damka mulki ga dan jam’iyyar APC.
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin cewa Fadar Shugaban Kasa ta maida wa Tunde Bakare raddi cewa Shugaba Muhammadu Buhari ba zai fidda wani dan takara daya ya ce shi ne zai gaji kujerar sa a zaben shugaban kasa na 2023 ba.
Kakakin Yada Labarai na Buhari, Femi Adesina ya ce duk da Buhari zai so a zuciyar sa a ce ga wanda zai gaje shi, “to ba zai fidda wani ya ce shi zai zama ‘halifan sa’ ba.”
PREMIUM TIMES ta buga labarin da Tunde Bakare ya shawarci ya shawarci Buhari ya fito da wanda ya ke so ya gaje shi a zaben shugaban kasa na 2023 da APC za ta tsaida takara, idan lokacin ya zo.
Bakare ya ce shugabannin kasashe irin su China, Singapore da Afrika ta Kudu duk su na fidda wanda zai gaje su tun kafin su kammala wa’adin su a kan mulki.
“Mu koyi darasi daga Nelson Mandela, wanda kafin ya sauka daga wa’adin zango daya, sai da ya tsaida Thabo Mbeki da Cyril Ramaphosa.”
Haka Bakare ya buga misali a shawarar da ya bai wa Buhari.
Bakare ya yi takarar shugaban kasa tare da Buhari a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa na Buhari, a zaben 2011.
Shi ne kuma Shugaban Cocin Latter Rain Assembly.
A martanin da ya bayar, Adesina ya yi magana a gidan talbijin na Channels ya ce, “Da yardar Allah cikin watan Mayu, 2023 Buhari zai kammala wa’adin sa na biyu, kuma wanda shi ne na karshe. Ba zai sake tsayawa takara ba. Wannan shi ne shirin da ke cikin zuciyar sa.
“Fasto Bakare y ace kamata ya yi Buhari ya bayyana wanda ya ke so ya gaje shi. Amma dai ba zai yi hakan ba. Ba kuma zai yi katsalandan a cikin tsarin da ya kamata a fitar da wanda zai fito takarar bayan sa ba.
“Shugaban Kasa ba zai fidda wanda zain zama ‘halifan sa’ ba. Mun san shi, ba irin mutanen da aa su wannan katsalandan din ba ne.
“Amma dai zai shiga tsamo-tsamo ya tabbatar da cewa an bi ka’idar duk da ta dace wajen yin zabe sahihi, ingantacce kuma karbabbe, wanda babu wanda za a bari ya shigo ya yi amfani da makudan kudade domin ya yi babakere ya zama dan takara.”
Adesina ya ce Buhari ba zai mika mulki ba ga wadanda za su maida Najeriya mugun halin da aka fiddo ta a ciki ba, ko kuma wadanda za su sake wawure dukiyar ba.
“A’a, hakan ba zai taba yiwuwa ko faruwa ba.”