A wani yunkuri da ake kallon neman karya lagon hayagagar masu adawa ce, Gwamnatin Jihar Kano ta kafa kwamitin da zai duba irin shirye-shiryen da kafafen yada labarai na cikin Jihar Kano ke watsawa, sannan a kafa musu iyaka da shingaye.
Kwamishinan Yada Labarai na Kano, Muhammad Garba ne ya bayyana haka, jiya Asabar, ga manema labarai, bayan tashi daga Taron Majalisar Zartaswa da aka gudanar.
Garba, wanda ya ce shi ne aka nada shugabancin kwamitin, zai ganq da shugabannin Hukumar Lura da Kafofin Yada Labarai (NBC), Hukumar Tace Finafinai, Ma’aikatar Shari’a, shugabannin gidajen Radiyo masu zaman kansu, bangarorin jami’an tsaro, jam’iyyun siyasa da Kungiyar ‘Yan Jarida ta Jihar Kano.
Ya ce za a shirya wannan taro ne domin a tattauna kalubalen da a ke fuskanta, tare da kawo mafita.
Jihar Kano dai ta fi sauran jihohin Arewa yawan gidajen radiyo masu zaman kan su.
Baya ga cewa wadannan kafafen yada labarai na bai wa ‘yan adawa fili su na caccakar gwamnatin Ganduje.
Wasu kuma na ganin cewa jami’an gwamnatin ba ta ji dadin yadda aka rika bada rahoton yadda ta karke a zaben cike -gurbi na
gwamnan jihar Kano, a cikin Maris, 2019 ba.
Wasu daga cikin gidajen radiyo masu zaman kan su a Kano, sun hada da Freedom Radiyo, Rahama Radiyo, Dala FM, Raypower FM, Pyramid Radiyo da sauran su.
A Kano ne aka fi yayata kwatagwangwama da kwamwcalar siyasa a Arewacin kasar nan, kuma da harshen Hausa.
Discussion about this post