KANNYWOOD: Zan karkata ga wasu harkoki baya ga fim a 2020 – Fati SU

0

Fitacciyar jarumar Kannywood Fati SU ta bayyana cewa daga yanzu za ta dan dauke kafa a harkar fina-finan Hausa zuwa dan wani lokaci domin ta fara wasu harkoki na ta.

A hira da tayi da PREMIUM TIMES a Abuja Fati ta ce ba wasan kwaikwayo bane za ta yi sallama da, tana nan sai dai kila ba kamar yadda aka saba ganin ta  a fina-finai ba.

” Taka rawa a wasan kwaikwayo ya zama jiki, ba zan iya cewa wai zan yi sallama da shi kwata-kwata ba. Zan rika fitowa amma ba yadda aka saba ganina kamar da ba.

” Dole mutum kuma ya dada jefa kallin sa a wani gefen domin yayi kamu mai kyau. Zan hada duk wani abu da zan yi wato sana’ a ko aiki da fitowa a fim ko da ko jifa-jifa ne.

Fati SU ta na fitowa a wasannin kwaikwayo na Hausa da da na Turanci sannan a shekarar da ta wuce ce ta kammala karatun digirinta ta biyu, a kwalejin kowar da sojoji, NDA dake Kaduna.

” Kila in iya fadawa aiki tsundum, kuma kaga idan hakan ya tabbata, zan rika samun karancin lokaci,
na fitowa a fim

Bayan haka jarumar ta nuna rashin jin dadinta ga yadda masu satar fasaha, wato ‘Piracy’ ya ne mi ya gurguntar da farfajiyar Kannywood.

” Matsalar masu satar fasaha ya yi matukar illata farfajiyar. Mai karamin karfi ba zai iya jurewa yin fim da sakawa a Sinema ba.

” Dole sai kana da jari mai kauri za ka iya yin tasiri a Kannywood yanzu. Domin don ka saka kudin ka ka yi fim, Zaka yi hasara  ne, saboda masu satar fasaha. Dole sai a Sinema kuma nan ma sai ka na da karfi.

Jarumar ta ce shugabanni da manya  a farfajiyar Kannywood din suna ta kokarin ganin a kawo karshen wannan matsala a farfajiyar.

A karshe Fati ta gode wa masoyan ta da sauran abokan aikinta cewa za su ci gaba da ganin farfajiyar ta ci gaba da daukaka a duniya baki daya.

Share.

game da Author