Tsohon Shugaban Kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida mai ritaya, ya ce kafa dakarun Ametokun da gwamnonin jihohin Yarabawa suka yi, ba daidai ba ne.
Babangida ya ce shiri ne wanda ba mai dorewa ba. Ya ce tunani ne mai kyau amma fa ba mai dorewa ba ne.
Babangida ya ce idan tafiya ta yi nisa, gwamnoni ba za su iya daukar dawainiyar tafiyar da rundunar ba.
“Ka ga dai tilas su samar musu kayan aikin da duk suke bukata. Za su ci gaba da biyan su albashi da sauran alawus da bukatun da suka wajaba a rika biya wa ma’aikacin jiha. To a ina a su rika samun kudaden daukar wannan dawainiya?
“Idan har suka yi nasarar gamsar da gwamnatin tarayya ta rika ba su wani dan kason kudi, to da dan dama-dama. Amma idan gwamnatin tarayya ta ce babu ruwan ta, to fa akwai matsala kwarai cikin lamarin.”
Haka Babangida ya bayyana a wata tattaunawa da aka yi da shi a Gidan Talbijin na Channels.
Babangida na ganin cewa har ma gara a kara inganta jami’an tsaro na sojoji, ‘yan sanda, NSC da sauran su, domin su tunkari kalubalen ake fuskanta a fannin tsaro a kasar nan.
Ba A Murkushe Boko Haram Ba
Babangida ya yi watsi da kakabin da gwamnatin tarayya ke yawan yi cewa an murkushe Boko Haram.
Ya ce idan aka yi la’akari da irin korafe-korafen da gwamnan jihar Barno, ya rika yi dangane da matsalar tsaro kwanan nan, to ganganci ne ma wani ya fito har ya rika cewa an murkushe Boko Haram.
“Maganar gaskiya sai fa an yi da gaske lamarin nan. Domin idan za mu yi la’akari da abubuwan da muke saurare a gidajen radiyo da wadanda muke karantawa a jaridu, kuma idan gaskiya ne, to akwai aiki tukuru a gaban mu fa.
“Ina ganin kamar ma akwai wasu mutane da ke juya tunanin su, su ke sanar da su komai, su ke musu komai. Akwai bukatar sanin wadanda ke musu tunani, su wa ke samar musu mugga kuma manyan makamai? To duk ya kamata mu dakatar da wannan. Ni dai nawa tunanin da hasashen kenan.”
Juyin Mulki Ya Zama Tarihi A Najeriya
Babangida ya kara da cewa ba zai taba yiwuwa a sake yin juyin mulki a Najeriya ba.
“Ai yanzu kwata-kwata babu ma wannan tunanin, kuma ba ma zai taba karbuwa a Afrika ba, har da sauran nahiyoyin duniya baki daya.
“Shi ma soja ya san idan ya yi juyin mulki, to duniya ba za ta karbe shi ba, kuma zai jefa kasar sa cikin yamutsi. Don haka ba ma zai fara yi ba.
Discussion about this post