A shekarar 2019 Hukumar Hisbah ta ta jihar Jigawa ta warware kullin auren
dole da aka yi wa ‘yan mata har 330.
Hukumar ta ce ta raba wadannan aurarraki ne a dalilin kin zama da wadannan mata suka yi a gidajen mazajen da aka yi musu auren dolen.
Shugaban hukumar Ibrahim Garki ya sanar da haka a hira da yayi da PREMIUM TIMES ranar Alhamis a garin Dutse.
Garki ya kara da cewa sai da ma’aikatan Hisbah suka gudanar da bincike masu zurfi kafin suka warware wadannan aurarraki na dole da aka yi wa wadannan mata. Sannan kuma sun gano cewa kusan mafi yawan su wadannan ‘yan mata ba su kai shekaru 18 ba ma aka yi musu auren.
Bayah haka ya ce hukumar da yi nasarar dakatar da wasu aurarrakin da da aka so ayi wa ‘yan matan ta karfin tsiya.
Daga nan ne kuma sai ya ci gaba da cewa baya ga aure, hukumar ta cafke wasu yara da ke yawon bara da sunan almajiranci sama da 436. ” Duk suna garararamba ne a tituna, sako sako, kurdi kurdi na jihar.”
“Muna kira ga iyaye da su bai wa ‘ya’yan su tarbiya ta gari tare da samar su ilimin boko domin guje wa fushin Allah a ranar gobe kiyama.