Iran ta sha alwashin ramuwar kisan da Amurka ta yi wa babban Janar din ta

0

A yanzu haka zaune ta tashi tsaye a fadin duniya, bayan da Amurka ta harbo jirgin da Janar Qasem Soleimani ke ciki, kuma ta kashe shi a harin.

Hedikwatar Tsaron Amurka Pentagon, ta tabbatar da kisan da ta yi masa tare da wani babban jagoran tawaye na kasar Iraki.

Soleimani shi ne Babban Kwamandan Zaratan Sojojin Iran na Quds Force, wadanda gogaggun sojoji ne na bangaren Dakarun Juyin Turu na Iran.

An harbo jirgin su ne a filin jiragen sama na Iraki, wanda shi ma Abu Mahdi ai-Muhadis, shugaban tawaye na Kungiyar Kata’ib Hezbollah da ake kira PMF na Iraki ya na cikin jirgin.

Wannan kungiya dai ta yi mummunar zanga-zanga a Ofishin Jakadancin Amurka da ke Iraki a ranar 31 Ga Disamba, 2010.

Ita ma Iraki ta yi Allah-wadai da kisan, tare da cewa zai kara haifar da rikici a kasar da kuma yankin baki daya.

Pentagon ta ce Shugaban Amurka Donald Trump ne ya bada odar a kai harin, a bisa zargin da Amurka ke yi cewa wadanda aka kashe din ke da hannu wajen tunzira jama’a yin mummunar zanga-zanga a ofishin jakadancin Amurka da ke Iraki.

Pentagon ta ce Amurka ta riki Sojojin da Soleimani da bangaren da al-Mahdi na Iraki ke jagoranci a matsayin kungiyar ta’addanci.

Pentagon ta kuma yi ikirarin cewa, “Soleimani na shirin shirya kai hare-hare a kan jakadun Amurka da ke Iraqi da kuma sauran kasashen Gabas ta Tsakiya.”

“Shi ne kuma ke da hannu wajen mutuwar daruruwan Amurkawa da sojojin kasar da dama, tare da raunata dubbai.”

Sanarwar ta kasa da cewa kisan na su zai zama darasi ga duk wanda ke da niyyar kai wa Amurkawa hari nan gaba.

Har yanzu dai Trump bai ce komai ba dangane da wannan kisa da Amurka ta yi, amma dai da safiyar yau Juma’a a ya tura sakon turkar Amurka a shafin sa na Tweeter.

A ranar 1 Ga Janairu dai an yi musayar yawu ta shafukan tweeter tsakanin Trump da Jagoran Musulunci na Iran Ayatollah Khameini, wanda ya ce Amurka na bata lokaci ta na zargin Iran a bisa kuskure, alhari ba gaskiya ba ne.

Daga nan ya ce ta’addancin da Amurka ke yi a kasashen Iraki da Syria ne ya sa al’ummar duniya suka tsane ta.

‘Za Mu Rama Kisan Da Amurka Ta Yi Wa Janar Soleimani -Ayatollah

Khameini ya fito a cikin talbijin din Iran a yau Juma’a ya na cewa Iran za ta rama kisan da Amurka ta yi wa Janar Soleiman a cikin kasar Iraqi.

Daga nan kuma sai ya yi sanarwar zaman makoki na kwanaki uku.

Haka shi ma Ministan Tsaron Iran, Amir Hatami, ya bayyana cewa Iran za ta yi abin da ake cewa ramuwar gayya, wadda wadda ta fi gayya zafi.

Haka dai gidan Kamfanin Dillancin Labarai na Iran, IRNA ya ruwaito.

A wani bangare kuma, China ta yi kiran da a kai zuciya nesa, yayin da kawunan Majalisar Amurka ya rabu biyu, da wadanda suka goyi bayan kisan da kuma wadanda suka yi tir da aikata kisan.

Share.

game da Author