Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya nemi majalisar dokokin jihar da ta amince wa gwamnati ta ciyo bashin Naira biliyan 15 domin inganta fannin ilimi a jihar.
Kakakin majalisar Abdulazeez Garba-Gafasa ya karanta wasikar neman bashin da gwamna Ganduje ya aiki a ranar Litini a zauren majalisar.
Garba-Gafasa ya ce Ganduje zai yi amfani da wadannan kudade ne wajen inganta ilimin boko kyauta a kananan hukumomi 44 na jihar.
Ya ce gwamnatin za ta biya bashin wadannan kudade ne daga cikin kason kudaden da gwamnati ke bata a duk wata.
Baya ga haka Garba-Gafsa ya gabatar da wasikar ga kwamitin harkokin kananan hukumomi na majalisar domin duba wannan himma na gwamnatin jihar.
Majalisar ta bai wa kwamitin kwanaki biyu ta mika rahoton ta.