Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, ta Kasa, INEC, ta bayyana rashin amincewa da janyewa shiga zaben da bai kammalu ba da Sanata Godswilll Akpabio ya yi, bayan ya zama Minista.
INEC ta shirya gudanar da zaben a Shiyyar Sanatan Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma, wanda zai gudana a ranar Asabar mai zuwa.
Cikin wata wasika da INEC ta aika wa Akpabio, Ministan Harkokin Neja Delta, a cikin Disamba, ta bayyana cewa ya makara da zai ce a yanzu ya janye shiga zaben, har ma ya nemi a canja sunan sa da na wani.
INEC ta ce ba zai yiwu a canja sunan wani ba, domin shi ne dai ya kai kara, kuma yanzu lokacin zaben ne, batun sauya sunan sa da na wani, kamar yadda ya nema ya shude tuni.
“Mun karbi wasikar da ka aiko, a ranar 10 Ga Disamba, inda ka nemi a canja sunan ka, a saka sunan Ekperikpe Luke Ekpo a matsayin madadin ka.
“Mu na sanar da kai cewa lokacin cire sunan wani a maida na wani, kamar yadda ka nema, to ya wuce tuni.”
Haka wasikar da INEC ta maida masa da amsa ta kunsa, kamar yadda Sakatariyar INEC, Rose Oriaran Anthony ta sa wa hannu.
“Don haka wannan zaben da za a kammala, zai gudana ne tsakanin wadanda suka shiga takarar sanatan kadai, domin haka dokar zabe ta gindaya.
“Don haka ba za mu iya karbar bukatar ka ta maye gurbin ka da wani ya fito takara a madadin kai da aka fara fafatawar da kai ba a Maris, 2019.”
Kokarin da Akpabio ya yi na komawa Majalisar Dattawa ya ci tura, yayin da Chris Ekpenyong na PDP ya kayar da shi a zaben 2019.
Ekpengyong ya yi mataimakin gwamna a Akwa Ibom, kamar yadda Akpabio ya yi mulki tsawon shekaru takwas daga 2007 zuwa 2015, a matsayin gwamnan jihar.
Ya koma APC daga PDP ana kusa da zaben 2019.
Bayan ya fadi zabe ne Shugaba Muhammadu Buhari ya nada shi Minista.
An nada shi minista bayan ya kai karar cewa an yi masa magudi. Bayan ya zama minista, sai ya bayyana cewa ya janye sake shiga zaben.
Ana ganin da wahalar ya yi nasara ko ma da ya sake shiga, ya ajiye kujerar ministadin, idan aka yi la’akari da wawar ratar da aka ba shi a zaben.
Da yawa na ganin gara ya tsaya a kujerar sa ta minista kawai maimakon ya sauka ya shiga zaben kuma ya yi biyu-babu.