Hukumar Kula da Canjin Yanayi ta Kasa (NiMet), ta fitar da hasashen yanayi da lokutan faduwar damina a cikin wannan shekara ta 2020, fadin kasar nan.
A cikin bayani da rahoton da NiMet ta fitar ranar Talata a Abuja, ta bayyana cewa a fara hasashen samun damina a yankunan Kudu Maso Kudu na kasar nan, tun a ranar 24 Ga Fabrairu.
Sannan rahoton ya ci gaba da cewa jihohi irin su Sokoto, Kebbi, Zamfara, Katsina, Jigawa da Barno, su yi tsammanin faduwar ruwan shuka daga ranar 2 Ga Mayu.
“A fara tunanin shigowar karshen damina tun daga ranar 26 Ga Satumba a Katsina da wasu sassa na Arewacin Sokoto, yayin da a yankin Neja-Delta kuma sai daga ranar 28 Ga Disamba za a fara ganin alamun karshen damina.
“Tsawon lokacin damina a cikin 2020 zai kai kwanaki 110 zuwa 160 a wasu yankunan sahel na Arewa, yayin da a Kudu kuwa zai kai kwanaki 210 zuwa 280.” Haka rahoton ya jaddada.
NiMet ta ce za a samu ruwan sama daidai-da-daidai, sannan kuma za a fuskanci lokacin da ruwan saman zai yi yawa fiye da yadda ake bukata.
Hukumar ta ce za a samu yawan ruwan sama a Arewa wanda ya kai yawan gejin ma’auni 400mm. A Kudu kuma yawan sa zai iya kaiwa gejin ma’auni har 3000mm.
Har ila yau, wannan rahoton ya nuna cewa za a iya samun yanayin da ruwan sama zai fara daga farko, daga nan kuma zai dauke zuwa wasu kwanaki masu yawa, kafin daga baya kuma daminar ta sauka ka-in-da-na’in.
A kan haka ne wannan hukuma ta shawarci manoma su guji sauri ko yin gaggawar shuka amfanin gona a farkon faduwar ruwan sama, gudun kada ruwan ya dauke zuwa wani lokaci har karancin ruwan ya sa su tabka asara.
Daga nan ne NiMet bayan farkon zubar ruwan shuka a farkon damina, za a fuskanci kwanaki kamar 10 zuwa 21 kafin ruwan ruwan sama ya sake zuba a jihohin Neja, Bauchi, Jigawa, Sokoto, Zamfara, Katsina, Kano, Kebbi, Yobe da kuma Barno.
Hakan a cewar hukumar zai faru tsakanin cikin watan Mayu zuwa cikin Yuni.
Discussion about this post