Hukumar Lafiya ta duniya WHO ta ayyana dokar ta baci kan cutar ‘Coronavirus’

0

Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya WHO ta bayyana cewa lallai dole a karkato kacokan don a daklie ci gaba da yaduwa da cutar coronavirus keyi tana mai cewa hakan babbar baraza na ce ga lafiyar mutanen duniya.

Ita dai wannan cuta tana dada yaduwa ne a kasashen duniya inda zuwa yanzu ta hallaka sama da mutane 100 a kasar Chana.

” An dauki wannan mataki ne saboda irin abubuwan dake faruwa a wasu kasashen duniya” Tedros Adhanom Ghebreyesus, da yake sanar da matakin ko kuma matsayar hukumar WHO a Geneva.

Tedros ya ce abinda ya fi tada musu hankali kuma ya sa dole a maida hankali wajen dakile yaduwar cutar shine gudun kada ta yadu zuwa kasashen da kiwon lafiyar su ke da matukar rauni, ‘musammam kasashen dake tasowa.’

Hukumar lafiya ta duniya ta ce mutum 98 sun kamu da cutar a wasu kasashe amma ba a samu mutuwa ba.

Akwai wasu mutane 8 da suka kamu da cutar a kasashen Jamus da Japan da Vietnam da Amurka.

Ghebreyesus ya kwatanta barkewar wannan cuta a matsayin babbar abin tashin hankali a duniya da ba a taba samun haka ba.

Majalisar dattawan Najeriya ta yi kira ga gwamnati ta kara ware kudade wa hukumar NCDC

A kasa Najeriya kuma majalisar dattawa ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kara ware kudade domin inganta aiyukkan da hukumar hana yaduwar cututtuka ke yi a kasar nan.

Majalisar ta yi wannan kira ne ganin yadda kwayoyin cutar ‘Corona Virus’ ke ta kara yaduwa a kasashen duniya.

Bayan nan kuma sai ta yi kira ga mutanen dake shirin tafiya kasar Chana da su dan dakata tukunna asamu saukin wannan cuta.

HANYOYIN GUJEWA KAMUWA DA CORONA VIRUS

1. A guji yawan cudanya da dabobbi.

2. Wanke hannu da ruwa da sabulu na da mahimmanci musamman bayan an taba dabbobi.

3. A rage yawan zama kusa da wadanda suka kamu da cutar.

4. A tabbata hannu na da tsafta kafin a taba ido, baki da hanci domin gujewa kamuwa da cutar.

Share.

game da Author