Hukumar EFCC ta gabatar da caje-cajen tuhumomi 19 a kotu biyu domin gurfanar da tsohon Mininstan Shari’a Mohammed Adoke a kotu.
Daga cikin caje-cajen har da wadanda suka danganci harkallar fitar da kudade, yi wa Najeriya kafar-ungulun kin samun makudan kudaden shiga da kuma zargin karbar cin hancin naira milyan 300.
PREMIUM TIMES ta ga kwafen tuhume-tuhumen da Adoke zai fuskanta a kotu, wadanda suka hada da tuhumar laifuka bakwai a Babbar Kotun Tarayya, Abuja, sai kuma wasu caji 12 da zai fuskanta a Babbar Kotun Abuja.
A tuhumar da ke gaban Babbar Kotun Tarayya, Abuja, akwai caje-cajen da suka hada da:
Karbar toshiyar baki daga wani dan kasauwa mai suna Abubakar Aliyu, har ta naira milyan 300 a cikin Satumba, 2012, a Abuja.
PREMIUM TIMES ta sha bayar da dalla-dallar rahoton harkallar Malabu, inda kusan rabin dala bilyan 1.1 kudin da aka sayar da Rijiyar Mai ta OPL 245 da kamfanonin Shell da Eni suka biya, aka karkatar da kudaden cikin asusun Abubakar Aliyu.
Shi ma Abubakar Aliyu din da shi EFCC ta hada ta maka kotu.
Abubakar shi ne hamsahakin dan kasuwar danyen mai mazaunin Abuja, da aka fi sani da AA Oil.
An dai bayar da rihiyar Malabu mai lamba OPL 245 ga Shell da Eni cikin 1998, ta haramtacciyar hanya.
An karkatar da sama da dala milyan 500 cikin asusun Abubakar Aliyu, a lokacin da Dan Etete ke Ministan Harkokin Man Fetur.
EFCC na zargin cewa an yi amfani da Abubakar Aliyu ya raba kudaden ga wasu jami’an Shell da Eni da kuma wasu jami’an gwamnatin Jonathan, ciki har da Adoke wanda ake zargin ya karbi naira milyan 300 cikin 2013, a matsayin kason sa na watandar kudin cinikin rijiyar mai lamba OPL 245.
Tuni dai aka fara tuhumar jami’an Shell da Eni a kotun kasar Italy.
Ana kuma tuhumar Adoke da bayar da naira naira milyan 347 da wani mai suna Usman, kamar yadda kwafen tuhume-tuhumen da ake yi masa a kotu mai lamba FHC/ABJ/CR/39/2017 ta nuna.
Cikin wasu tuhume-tuhumen da ake wa Adoke a Babbar Kotun Abuja kuwa, har da karbar toshiyar baki daga Shell da Eni, sai hada baki da shi a damfari Najeriya, ta hanyar daga wa Shell da Eni kafar kin biyan haraji sai shirya harkallar amincewa da adadin kudaden da za a biya Najeriya.
Makonni uku da suka gabata ne Adoke ya dawo daga Dubai, inda jami’an EFCC suka yi cacukui da shi tun daga filin jirgin sama na Abuja.
Har yanzu kuwa ya na hannun su, domin bayan ya shafe kwanaki, sai EFCC ta sake garzayawa kotu, ta karbi sammacin amincewa ta ci gaba da tsare shi har tsawon kwanaki 14.
A kotu ne yanzu za a ji shin kurkuku za a auna shi, ko kuwa beli zai yi saurin nema tun ba a kai shi kurkuku ba.