HARKALLAR DALA BILYAN 1.2: Kotu ta bada belin tsohon minista Adoke

0

Babbar Kotun Abuja da ke Gwagwalada, ta bada belin tsohon Ministan Shari’a, Mohammed Adoke a kan naira milyan 50.

Ana zargin Adoke da shiga tsakani wajen yin dillancin harkallar dalabilyan 1.2 da aka yi cinikin wata rijiyar mai.

Mai Shari’a ne ya bayar da belin Adoke tare da umartar sa ya gabatar da mai tsaya masa, wanda zai tabbatar da cewa sai mazaunin Abuja.

Bayan nan kuma Mai Shari’a Kutigi ya ce mazaunin Abuja din ya kasance ya na da kadarar gida ko wani babban fili a Abuja.

Wanda ake zargin su tare din, wato Abubakar Aliyu, shi ma an bada belin sa a kan naira milyan 50.

Mai Shari’a ya ce wa Aliyu, wanda gawurtaccen attajiri ne mai harkar mai a Abuja, zai gabatar da mai beli wanda zai kasance ya na gida ko babban fili a Abuja. Kuma zai ajiye naira milyan 50.

Na uku din da ake tuhuma tare da Adoke kuwa, an nemi a ajiye naira milyan 10 a matsayin kudin belin sa.

Ana zargin Adoke da karbar naira milyan 300 a matsayin toshiyar baki daga cikin kudin cinikin rijiyar.

Sannan kuma ana zargin sa da shirya kakudubar da ta yi sanadiyyar aka saida rijiyar a farashi mai rahusa, wadda hakan ya janyo wa Najeriya asarar dimbin makudan kudade.

An dai sai da rijiyar ce mai lamba OPL 245 ga kamfanonin mai na Shell da Eni da ke Najeriya.

Rabin kudin, wato dala milyan 600 duk an karkatar da su ne asusun Abubakar Aliyu, wanda shi kuma ya rika watandar kudaden ga sauran ’yan harkallar.

Share.

game da Author