HARKALLAR CACA: EFCC ta garkame babban kartagin Najeriya

0

Hukumar EFCC ta damke Segun Adebutu, babban kartagin ’yan cacar Najeriya, bisa zargin harkallar bilyoyin nairorin da kamfanin cacar sa ya ki biyan gwamnati haraji.

Adebutu, wanda aka fi sani da ‘Baba Ijebu, shi ne babban dan Kessington Adebutu, kasurgumin dattajijon da ya assasa cacar lotare ta wannan zamani a Najeriya. An damke shi a Lagos ranar Talatar nan, inda jami’an EFCC ke ci gaba da yi masa tambayoyi a kan zargin zambatar gwamnati bilyoyin nairori wajen kin biyan haraji.

Haka dai PREMIUM TIMES ta tabbatar cewa an kama shi a yau a Lagos.

An kama dan babban kartagin kamfanin caca na Premier Lotto, bayan da wani kamfanin cacar mai suna Western Lotto ya kai wa EFCC korafi a rubuce cewa Premier Lotto baya biyan haraji ga gwamnati har tsawon wani lokaci.

PREMIUM TIMES ta ga kwafen takardar korafin, kuma wata majiya ta tabatar da cewa ya zuwa yanzu EFCC ta samu bayanan da suka nuna cewa akalla sun gano jami’an kula da kamfanin cacar Premier Lotto sun ki biyan akalla har naira bilyan 5 da suka janyo wa gwamnati asarar rashin samu.

Tsohon Sanata Buruji Kashamu ne babban kartagin kamfanin caca na Western Lotto, kuma kamfanin ne ya kai korafin Premier a Hukumar EFCC.
EFCC da Adebutu dai ba su amsa kiran PREMIUM TIMES ba, domin a ji ta bakin kowane bangare.

An yi wa kamfanin cacar lotare na Premier Lotto rajista a cikin 2001. Segun Adebutu da aka damke a ranar Talata kuma na daya daga cikin akalla ’ya’ya hudu na Kessington Adebutu, uban ’yan cacar Najeriya da ke shugabancin kamfanin cacar wanda ya shahara sosai a fadin kasar nan.

Wasu daga cikin ’ya’yan ma na cikin Hukumar Kula da Cacar Lotare ta Tarayya.

Ganin irin makudan kudaden da ake samu a harkar cacar lottery ce ta sa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya kafa hukumar da za ta rika kula da harkokin cacar lotare a Najeriya.

Tun daga lokacin ne sai harkar ta bunkasa sosai, inda akasafi a kan wasannin kwallon kafa ne ake yin cacar.

‘Caca Fi Harkar Fetur Kawo Kudi’

Sai dai kuma baya ga Premier Lotto, wakilin mu ya tabbatar da cewa EFCC na binciken wasu kamfanonin cacar da dama, bisa zargin harkallar makudan kudade da ta hada har da rike kudaden wadanda suka ci caca, domin su rika samun riba a bankuna.

Wata majiya da ke da masaniyar yadda wannan bincike ke tafiya, ta tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa ana samun makudan kudade a harkar cacar, “kusan za a iya cewa ma ta fi harkar man fetur kawo kudi.”

“Mun kuma gano cewa Buruji Kashamu ya ce shi ne mai kamfanin cacar lotto mai suna Ghana Games’ a Nijeriya.

Sai dai wannan jami’in y ace kungiyar Manyan Kartagin ’Yan Cacar Najeriya za su hadu su yi wa EFCC jawabin bai daya, dangane da takardar korafin da kamfanin Buruji Kashamu ya aika wa EFCC.

Kashamu: Biri Tafi Da Hagun Ka…

Buruji Kashamu ya gudo daga kasar Amurka ne bayan da aka kada kararrawar neman sa, bisa zargin sa da harkar safarar kwaya. Duk da haka bayan da ya dawo Najeriya, sai da ya tsaya zabe, har ya zama sanata.

A hirar sa da PREMIUM TIMES, ya ce shi bai aikata wani laifin komai a Amurka ba.

Dangane da koken da ya kai wa EFCC kuwa a kwanan nan cikin Disamba, a kan zargin Premier Lotto sun karkatar da makudan kudaden haraji, an zargi Kashamu da cewa ya na nukura da Premier Lotto ne, saboda ya kashe masa kasuwa, kamfanionin sa na Western Lotto da Ghana Games ba su da nasibi sosai a yanzu.

A wannan zargin ma Kashamu ya ce ba haka ba ne, shi dai ya yi ne kawai domin gwamnati ta tsaftace harkar cacar kawai.

“Kudaden harajin da Premier Lotto ya ki biyan Hukumar Kula da Harkar Cacar Lotare ta Tarayya, sun isa a yi wa jama’a ayykan raya kasa masu tarin yawa.” Cewar Kashamu, a hirar da PREMIUM TIMES.

Share.

game da Author