Idan ba a manta ba a daren Talata ne mahara dauke da manyan bindigogi suka tare tawagar sarkin Potiskum a titin Kaduna zuwa Zaria.
Wannan hari yayi sanadiyyar rayukan mutane akalla 30 sannan kuma maharan sun yi garkuwa da mutane 100.
Gwamna Mala Buni na jihar Yobe ya bayyana cewa wannan abu ya tada masa da hankali matuka sannan yayi kira ga jami’an tsaro da su kara kaimi wajen sama wa mutane tsaro a ko ina a fadin kasar nan.
Sarkin Potiskum Umara Bauya, ya fada wa shingen da maharan ne da misalin karfe 11 na daren Talata inda maharan suka budewa jerin motocin sa wuta sannan suka har suka kashye direba daya da dogarai 3.
An yi jana’izar wadannan dogarai a fadar sarkin a Potiskum, shi kuma sarkin na nan kwanci a wani asibiti ana duba shi a garin Kaduna.
Shugaban sarakunan jihar Yobe, Sarkin Fika Muhammadu Idrissa, ya mika ta’aziyyar sa ga iyalan wadanda suka rasa rayukan su a wannan hari sannan shima yayi kira ga jami’an tsaron kasar nan da su kara zage damtse wajen fatattakar wadannan mahara.
Ya koka kan yadda rashin tsaro ya zama ruwan dare a kasar nan inda ake ta rasa rayuka da dukiyoyi a sanadiyyar harin mahara da masu garkuwa da mutane.