Dubban ‘yan kasar Iran ne suka fito manyan titunan kasar a sassa dabam dabam domin yin zanga-zangar nuna fishin su kan harbo jirgin saman Ukraine da makami mai linzami da sojojin kasar suka yi.
Kamfanin dillancin labarai ta IRNA da Isna sun ruwaito cewa mutane da dama sun yi Allah-Wadai da harbo wannan jirgi.
Mutane da suka yi hira da IRNA sun bayyana cewa dole mutanen kasar su fusata kan abin da gwamnatin kasar ta yi.
” Muna kira ga duk wanda ke da hannu a wannan abu ya yi murabus kawai. Mu wannan abu da gwamnati ta yi bai yi mana dadi ba ace a harbo jirgi dauke da daruruwan mutanen da basu ji ba ba su gani ba.
Bayan haka, shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa dole a rika bari mutane na yin zanga-zanga akan abinda bai yi musu dadi ba a kasar. Ya ce za su sa ido su gani ko gwamnati za ta tauye wa mutane hakkin su na damar yin zanga-zanga.
Sannan a kasar Birtaniya kuma, ministan harkokin wajen kasar ya yi tir da tsare jakadan kasar da jami’an tsaron kasar Iran suka yi na tsawon awa daya a kasar.
Jami’an tsaron kasar Iran sun tsare jakadan kasar Britaniya a kasar saboda ya fito yin zanga-zangar harbo jirgin Ukraine da kasar Iran ta yi.
A ranar Juma’a ne kasar Iran ta lashe aman ta bayan ta musanta cewa ba ita ce ta harbo jirgin Ukraine.
Kasar ta ce ta harbo wannan jirgi ne a bisa kuskure ba da gangar ba.
Fasinjoji 176 ne suka mutu a wannan jirgi. Mafi yawan fasinjojin ‘yan kasar Canada, sai Jamus da Birtaniya.
Akwai akalla ‘yan kasan Iran 80 da suka rasu a wannan hadarin jirgi.