HANDAME KUDADEN MA’AIKATA: Tsohon Kwamishina zai yi zaman gidan kaso na shekaru 19

0

Babbar kotu dake Okene jihar Kogi ta yanke wa wani tsohon kwamishinan aiyukkan noma na jihar Zacchaeus Atte hukuncin zama a gidan kaso na tsawon shekaru 19 bayan an same shi da laifin cin ye wasu kudaden ma’aikatar sa.

Alkali kotun J.J Majebi ya daure Atte bisa ga laifuka Bakwai daga cikin laiffuka 11 da hukumar ICPC ta shigar a kotun.

Da yake karanta hukunci da kotun da yanke, Majebi ya ce Atte zai yi zaman gidan kaso na tsawon shekaru Biyar kan aikata laifin sace Naira 11,937,000:00 da 8,873,766:85 da aka ware domin siyowa da raba irin kwakwan manja ga manoman Coco dake jihar.

Alkalin ya kuma ci gaba da cewa Atte zai yi zaman gidan kaso na tsawon shekara Biyar a dalilin kama shi da laifin yin sama da fadi da Naira 350,000 da aka ware domin biyan kudin motan wadannan manoma da suka zo karban irin kwakwan.

Sannan zai yi zaman shekara daya a dalilin aikata laifuka guda Tara wanda a ci akwai sace Naira 2,849,953:75 da aka ware domin siyo kujeru da sauran kayan aikin Ofis wanda a cewar Atte wai ya kashe wadannan kudade ne a yawon bude ido zuwa jihohin kasar nan sannan da biyan mai daukan bidiyo a yawon.

A takaice dai za a daure Atte na tsawon shekaru 19 ba tare da an bashi damar beli ba.

A karshe hukumar ICPC ta nuna gamsuwarta da hukuncin da kotun ta yanke.

Share.

game da Author