Gwamnatin Najeriya ta horas da manoma mata dabarun tattalin kudi

0

Ma’aikatar aiyukkan noma da ci gaban yankunan karkara ta bayyana cewa gwamnati ta tsara wani muhimmin shiri don horas da mata manoma 80 da aka zabo daga shiyyoyi Shida a kasar domin koyar dasu dabarun tattalin kudi.

Shugaban sashen bunkasa aiyukkan noma na ma’aikatar ayyukan gona, Karima Babangida ta bayyana haka a Abuja.

Karima ta ce gwamnati ta tsara wannan shiri ne domin wayar da kan mata manoma musamman wadanda ke a karkara kan yadda za su iya samun jari domin bunkasa sana’ar noman da suke yi sannan da yadda za su iya yin tattalin ribar da suka samu don bunkasa ayyukan su.

Ta ce horas da mata kan dabarun tattalin kudi a harkar noma zai taimaka wajen bunkasa aiyukkan noma, samar da abinci a kasa sannan da samar da aikin yi ga mutane musamman mata.

Karima ta kuma kara da cewa da zarar an kammala shirin gwamnati za ta baiwa kowacce mace satifiket da zai taimaka wa mata wajen samun bashi daga tsarin inganta aiyukkan noma da kasuwanci ta babbar bankin Najeriya (AGSMEIS).

Baya ga haka shugaban kungiyar mata na Najeriya Hadiza Umar da sakatariyar kungiyar mata namoma da ‘yan kasuwa (AWITA) Jima Mariatu sun ce shirin zai taimaka wa mata wajen cin gashin kansu musamman ga matan dake sha’awar shiga harkar kasuwanci.

“ Tabas wannan shiri zai taimaka wa mata wajen samun jari, yin tattali kudaden su da inganta rayuwar su”.

Idan ba a manta ba a watan Nuwanbar 2019 ne Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da shirin kara jawo mata a cikin harkokin noma da yadda za su rika samun tallafi da karfi daidai da maza.

Ministan Harkokin Noma, Sabo Nanono ne ya bayyana haka inda ya kara da cewa manufa da muradin shirin shi ne a bayar da dama daidai ha kowane jinsi na maza da mata domin a bunkasa samar da abinci a cikin kasa.

Share.

game da Author