Gwamnatin Jihar Zamfara ta ce za ta gina sabon gidan gwamnati da zai yi daidai da gidajen gwamnatocin na zamani.
Sakataren gwamnatin jihar zamfara Bala Bello, ya bayyana haka da yake yin bayani kan kasafin kudin 2020 na jihar.
” Idan ba a manta ba gidan gwamnati da muke yanzu a ciki shine sakatariyar karamar hukumar Gusau a lokacin da jihar ke tare da lardun Sokoto.
” An ari wannan sakatariya ne domin zama gidan gwamnati na wani dan lokaci tub a 1996 da aka kirkiro jihar.
Jihar Zamfara na bukatar sabon gidan gwamnati irin na zamani kamar yadda sauran jihohi suke tunkaho da. Idan har Allah yasa aka kammala wannan gida, za a maida wadda ake yanzu a ciki karin ofisoshin gwamnati da dama ake karancin su.