Gwamna Zulum ya fusata ga yadda sojoji ke karbar kudade daga hannun matafiya

0

Gwamnan Jihar Barno, Babagana Zulum, ya zargi sojoji da ‘yan sandan da ake girkewa a kan titina sun a karbar naira 1000 daga matafiyan da ba su da katin shaidar dan kasa.

Zulum ya yi wannan zargi ne yau Litinin a lokacin da ya kai ziyara kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu, inda dubban matafiya suka yi tsaye cirko-cirko a daidai inda sojoji suke binciken masu wucewa su shiga Maiduguri.

Wannan babbar hanya dai ita kadai ce hanyar shiga da fita daga cikin Maiduguri, duk kuwa da irin hare-haren da Boko Haram suka rika kaiwa a kan titin kwanan nan.

Yayin da gwamna ya isa daidai shingen sojoji da ‘yan sanda da ke kusa da Jami’ar Maiduguri, sai ya ci karo da daruruwan motoci sun yi layi daga kowane bangare na titin.

“Ba za a ci gaba da lamuntar irin wannan abu ba.” Haka Zulum ya rika nanatawa da karfin murya.

“Ta yaya za ku rika azabtar da jama’a irin da sunan wai binciken katin dan kasa?

“Ko tausayi ba ku ji, kun maida hankula wajen karbar naira 500 da naira 1000 daga talakawan da ba su da katin dan kasa.”

Yayin da wani soja ya yi korarin yi wa gwamnan bayani, sai Zulum ya ce, “A’a, wannan dai ba daidai ba ne, gwamnatin tarayya ba ta samar hanya mai saukin da kowa zai samu katin dan kasa ba. Ku kuma ku na nan ku na karbar naira 500 da naira 1000 a matsayin kudin tara ga wanda ba shi da abin da gwamnatin tarayya ta kasa samar masa.”
Gwamna Zulum ya ce masu ya sha karbar rahoton yadda sojoji ke karbar kudade a hannun matafiya.
Daga nan sai Zulum ya sa hadiman sa su kira Kwamandan Yaki da Boko Haram, Janar Olusegun Adeniyi.
Bayan an kira shi ya amsa, an ga Zulum ya karbi waya, kuma aka ji shi ya na cewa, “Theater Commander ka na ina ne? … ni a yanzu ga ni nan tsaye a shingen da sojoji ke binciken matafiya, kuma ga dubban matafiya sun yi tsaye cirko-cirko, mutanen ka na karbar kudade ga wadanda ba su da katin dan kasa. Saboda me?”

Nan da nan Zulum ya bada umarni a bude hanya duka bangarorin biyu, kowa ya wuce.
Wasu matafiya sun shaida wa manema labarai cewa sun dade tsawon sa’o’i da dama a wurin, ba tare da an ce musu komai ba.
“Na bar Damaturu tun karfe 9 na safe. Na iso nan wajen karfe 11, amma ga ni a tsaye har yanzu karfe 3 na yamma.” Haka wani direban bas da ya ce sunan sa Isa Adamu ya shaida wa wakilin mu.
Wata mata da ta taso da daga Bauchi za ta Maiduguri, ta ce “an umarci na biya naira 500, saboda ba ni da katin dan kasa, amma ba ni da ko sisi, domin na kashe dan abin da na rage daga guziri na a Damaturu, inda kwana ya kama mu a can. Saboda sojoji sun ce ba za mu iya shiga Maiduguri bayan karfe 5 na yamma ba.”
Daga baya Adeniyi ya je wurin, inda ya bayyana cewa tara dandazon jama’a a wurin ba sojojin ne suka haddasa shi haka kawai ba. “Al’amarin inji shi ya faru ne saboda Boko Haram sun kai wani hari a ranar.”
Ya kuma ce zai binciki zargin da aka yi kuma zai bayyana komai idan har gaskiya ne.
Zulum ya ce da gaske ne. “Da ido na ni ma na ga suna karba, kuma na yi magana da wasu daga cikin mutanen da aka ce sai sun biya kudi!”
A nan dai aka rika cacar baki da Janar Adeniyi da Gwamna Zulum, wanda ya bar wurin a fusace, ya yi gaba zuwa Jakana, kauyen mai mai tazarar kilomita 45 daga Maiduguri, inda Boko Haram suka kai hari cikin makon da ya gabata.
“Ya zama dole ka san cewa gwamnati da al’ummar jihar Barno ta na bayan kai da sojojin ka, amma kuma dole ya tsawatar wa sojoji daga karbar kudade da suke yi a hannun jama’a.”

Share.

game da Author