Gwamna Lalong ya tsallake siradin Kotun Koli

0

Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong ya zama cikin gwamna na hudu da suka tsallake siradin Kotun Koli a yau Litinin.

A shari’ar da gaba dayan alkalan bakwai suka amince, sun jaddada nasarar Lalong da Kotun Daukaka Kara ta bayyana.

Kotun Koli a yau ta ce babu wani hurumin da zai sa dan takarar PDP na jihar Filato, Jeremiah Usaini zai kai kara, domin bai ci zabe ba.

A yau Kotun Koli ta jaddada Abdullahi Ganduje na Kano, Aminu Tambuwal na Sokoto da kuma Bala Mohammed na jihar Bauchi.

Tun bayan fara shari’un gwamnoni, har yau na jihar Imo ne kadai aka tsige. Shi ma din ana ya ce-ce-ku-ce cewa an yi mamakin yadda aka kwace daga hannun PDP aka bai wa dan APC, wanda, wanda ya zo na hudu.

Yanzu dai kallo ya koma kan yadda PDP ke zanga-zangar bukatar Kotun Koli ta maida musu kujerar Gwamnan Jihar Imo.

Share.

game da Author