GOBARA: Magidanci ya rasa matarsa da ‘ya’yan sa mata uku a jihar Yobe

0

Hukumar kashe gobar ta jihar Yobe ta bayyana cewa gobara ta wasu mutane hudu a jihar.

Shugaban hukumar Usman Habu ya sanar da haka da yake hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Laraba a garin Damaturu.

Habu yace wannan abin tashin hankali ya auku ne ranar Talata da kafe 11 na dare.

Ya ce gobarar ta tashi a gidan Malam Adamu Aliyu dake zaune a kwatas din ‘Red Bricks’ dake hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

Habu ya ce Malam Aliyu da dansa Faruq Aliyu mai shekaru biyar ne kadai suka tsira da rayukan su.

“ Mun samu labarin tashin gobara a kwatas din Red Bricks inda bayan mun iso wurin sai muka taras da Malam Aliyu da dansa Faruq a wajen gidan su su saka wa ikon Allah ido.

“ Matar Aliyu da ‘ya’yan sa mata uku sun riga mu gidan gaskiya duk da kokarin ceto su da ma’aikatan mu da Malam Aliyu suka yi.

Ya yi kira ga mutane da su riki yi kofar fita ta gaggawa domin guje wa irin haka nan gaba.

“ Sannan a guji ajiye duk abubuwan da zasu iya tada gobara a gida tare da kashe duk kayan wutan lantarki idan za a fita gida.

Binta Mohammed makwabciyar gidan Malam Aliyu ta ce ‘ya’yan Aliyu da suka rasu a sanadiyar gobarar sun hada da Aisha Aliyu mai shekaru 10, Saadatu Aliyu da Safiya Aliyu dake da shekaru biyu.

Share.

game da Author