Fulani a yankin Filato sun yi tir da kisan da wasu mahara suka yi wa mutane 13 da bindiga, a kauyen Kwatas, cikin Karamar Hukumar Bokkos a ranar Lahadi.
Sai dai kuma Fulanin sun yi kukan cewa wasu da suka kai harin da ake ganin cewa kamar na ramuwar gayya ne, sun kai wa gidajen Fulani hari, suka kone da dama kurmus.
Shugaban Miyetti Allah na Jihar Filato, Isa Bappa ya bayyana haka a ranar Talata a wani taro da manema labarai a Jos, babban birnin jihar.
A wannan rana dai ce shi ma Gwamna Simon Lalong ya ce lallai sai jami’an tsaro sun kamo dukkan wadanda ke da hannu wajen aikata kisan.
Lalong ya gana ne da jami’an tsaro da kuma shugabannin yankunan karkara na gargajiya.
Bappa ya ce, “Abin bakin ciki ne ganin yadda bayan wancan hari da wasu suka kai a kauyen Kwatas, sai kuma matasan kauyen suka fusata, suka rika bin gidajen Fulani su na konewa. Dukkan wadannan hare-hare biyun dabbanci ne.
“Mu na kira ga jami’an tsaro a wannan jihar su gaggauta kamo dukkan wadanda ke da hannu a wadannan hare-hare.
“Sannan kuma bain bakin ciki ne da muka karanta a wasu jaridu cewa Rundunar ‘Yan Sandan Filato ta fada a ranar 27 Ga Janairu cewa wai Fulani makiyaya ake zargi da kai harin.”
Bappa ya ce ‘yan sanda sun yi gaggawa da azarbabin dora wa Fulani laifin kisa, “saboda babu wata hujjar da ke nuna cewa Fulani ne suka kai hari a Kwatas.”
“Mu na kira ga jami’an tsaro cewa a koda yaushe su rika yin kyakkyawan nazari kafin su yi gaggawar bayyana batun da ba su da tabbas a kan sa.”
Wata Kunyar Fulani ta Gani Allah Association, ta ce an kone gidajen Fulani 23 da kuma wani masallaci guda daya a harin da matasan kauyen suka kai wa rugar Fulani.
Haka kakain kungiyar Abubakar Yunus ya bayyana.
Shi kuwa gwamna Lalong, ya yi kira ga jami’an tsaro cewa su kamo dukkan wadanda ake zargi da aikata kisan.
Ya kuma umarce su da su kamo shugabannin Fulani da Ardo-ardon da ke yankunan, su tasa su gaba sai sun kai su wurin da wadanda duk ake zargin su ke an kamo su
Discussion about this post