Hukumar inganta abinci da magunguna (FDA) ta amince da sabuwar maganin kawar da ciwon zuciya da aka sarrafa shi da man kifi.
FDA ta amince da wannan magani ne bayan tabbatar da ingancin sa da kuma domin sama wa masu fama da ciwon zuciya saukin samun magani.
Hukumar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya (CDC) ta bayyana cewa ciwon zuciya na daga cikin cututtukar dake kisar mutane da dama sannan har yanzu cutar na ci gaba da yaduwa a duniya kamar wutan daji.
Hukumar ta ce a dalilin haka yake da mahimmanci wajen samar da maganin da zai taimaka wajen dakike yaduwar cutar.
Idan ba a manta ba a watan Oktobar 2019 Kungiyar likitoci na (NCS) ta koka kan yadda cutar hawan jini ke kama mutane a Najeriya.
Kungiyar ta koka da haka ne a taron samar da madafa kan yadda za a shawo kan yaduwar cutar a kasar nan da aka yi a jihar Enugu a wancan lokaci.
NCS ta ce bincike ya nuna cewa akalla kashi 30 bisa 100 na mutanen Najeriya na fama da cutar.
Binciken ya nuna cewa matasa musamman masu shekaru 25 na daga cikin yawa-yawan mutanen dake kamuwa da wannan cuta a kasar nan.
NCS ta yi kira ga mutane da su kiyaye hanyoyin guje wa kamuwa da cutar.
Wadannan hanyoyi kuwa sun hada da:
1. Mutum ya yawaita motsa jiki domin rage kiba a jiki
2. A rage yawan cin Kitse, sannan a yawaita cin kayan lambu da ganyayyaki.
3. A rage shan kayan zaki
4. A rage yawan cin gishiri.
5. Shan taba sigari da shan giya na kawo cutar hawan jini.
6. A yawaita zuwa asibiti domin yin gwaji akan cutar.
Discussion about this post