EFCC na bibiyar kadarori na don kawai ta cusa min bacin rai ne – Inji Saraki

0

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya nemi Babbar Kotun Tarayya da ke Lagos ta yi fatali da karar sa da EFCC ta kai, inda hukumar ta nemi kotun ta ba ita EFCC din ikon kwace wani gidan Saraki da ke Ilorin, Babban Birnin Jihar Kwara.

Cikin watan Disamba ne dai EFCC ta samu damar-wucin-gadi na rike gidan na Saraki, har zuwa yadda shari’a ta kaya a kotu.

Gidan wanda ke a Lamba 1, Abdulkadir Street, EFCC ta nemi kwace shi ne a bisa zargin cewa da kudaden harkalla Saraki ya saye shi.

Mai Shari’a Rilwan Aikawa dai a cikin Disamba ya bai wa EFCC takaitaccen ikon kwace gidan, kafin a ga yadda shari’a za ta kaya tukunna.

Sai dai kuma a wata kara da Saraki ya shigar ta hannun lauyan sa, Kehinde Ogunwumji, ya ce abin da EFCC ta yi masa a waccan kotun, karya ka’idar da doka ta tsara ne, kuma wani hardadden kulli ne EFCC ta shirya domin ta bakanta kuma ta yi wa Saraki yamadidi a duniya, domin ta kunyata shi.

Cikin karar da Saraki ya shigar main lamba FHC/L/CS/1867/2019, lauyan sa Ogunwumji ya ce an karya dokar da shari’a ta gindaya a lokacin da waccan kotun ta bai wa EFCC ikon rike gidan na wani lokaci.

Saraki ya tunatar da Babbar Kotun Tarayya cewa tun a ranar 6 Ga Yuli, 2018 ne Kotun Koli ta sallami karar da aka gurfanar da shi.

Don haka Saraki ya ce babu wani dalilin da EFCC za ta sake yin wani azarbabin rike masa wani gida kuma a yanzu.

Daga nan sai ya roki Mai Shari’a Aikawa da ya kori karar da EFCC ta shigar, kuma ya umarci hukumar ta sakar masa gidan sa na Ilorin da ta rike.

Shi kuma lauyan EFCC ya ce hukumar ta samu rahoton da ke nuna cewa da kudin harkallar da Saraki ya tara ya sayi gidan, a lokacin da ya ke gwamnan jihar Kwara, tsakanin 2003 zuwa 2011.

Share.

game da Author