Duk da ko rantsar da shi ba a yi a majalisa ba, sunan Yari da wasu sanatoci sun bayyana a shafin ta na yanar gizo

0

Duk da cewa ko rantsar dashi ba a yi a majalisa ba, sunan tsohon gwamnan jihar Zamfara, AbdulAziz Yari na nan daram a shafin majalisar dattawa a yanar gizo.

Ba shi kawai ba, akwai wasu sanatocin da duk kotu ta tsige su daga kujerun su amma ba a iya cire sunan su a shafin majalisar ba.

Baya ga Yari wanda shafaffe da mai ne, da ko rantsar da shi ba a yi ba a majalisar ballantana ace wai har an saka shi a shafin majalisar a matsayin Sanata akwai Sanata Dino Melaye.

Shi ma Sanata Dino Melaye ya fadi zaben kujerar sa da aka sake yi. Amma kuma ba a musanya sunan sa da Smart Adeyemi ba.

Shi ma Adedayo Adeyeye daga jihar Ekiti da aka tsige sunan sa na nan a shafin majalisar.

Sannan kuma akwai Abubakar Tambuwal, daga jihar Sokoto, Tijjani Kaura da Christopher Ekpenyong.

Shi kuma Benjamin Uwajumogu da ya riga mu gidan gaskiya, shi ma har yanzu suna da hoton sa shafin majalisar dattawa dake yanar gizo.

PREMIUM TIMES ta nemi ji daga bakin masu ruwa da tsaki a majalisar musamman sashen da ke kula da shafin da sunayen sanatoci suke amma basu ce komai ba akwai.

Share.

game da Author