Hukumar tabbatar da ingancin makarantu na jihar Kaduna ta bayyana cewa daga cikin makarantun firamare da sakandare masu zaman kansu 4,000 dake jihar 2,000 ne kadai suka iya yin rajista bayan tilasta musu da gwamnati ta yi a cikin shekarun baya.
Shugaban hukumar Hajiya Umma Ahmad ta fadi haka a hira da tayi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Kaduna ranar Litini.
Umma ta ce hukumar ta bankado wasu makarantun da dama da suka shekara sama da ashirin suna aiki amma basu da rajista sannan basu taba biyan haraji ba.
“Shekarun baya da suka wuce makarantu 1,000 ne ke da rajista a jihar nan da hakan ya sa gwamnati ta fara rufe duk makarantar da bata da rajista a jihar.
“Bayan haka ne makarantu da dama suka garzayo domin ayi musu rajista.
” Gwamnati za ta ci gaba da farautar wadannan makarantu a jihar.
Umma ta kuma ce gwamnati za ta fitar da jadawalin jerin sunayen makarantun firamare da sakandare masu zaman kansu da suka inganta a yanar gizo saboda iyaye su rika sanin makarantun da suka fi dacewa da ‘ya’yan su.
“Nan ba da dadewa ba gwamnati za ta fitar da jerin sunayen makarantun firamare da sakandare a jihar domin iyaye su rika tantance makarantun da za su rika saka ‘ya’ya.
Discussion about this post